Mai Shari’a Taiwo Taiwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya amsa rokon da EFCC ta yi masa cewa a ba ta ikon kulle asusun ajiyar Gwamnatin Jihar Bauchi har sai bayan ta gama bincike.
Asusun da EFCC ta kulle din dai na ajiyar kudaden gwamnatin jihar Bauchi ne da ke ajiye a bankin FCMB mai lamba 0998552024.
Lauyan EFCC Abubakar Aliyu ne ya roki a bai wa EFCC ikon kulle asusun har sai hukumar ta kammala binciken yadda aka yi asarkalar fitar da naira bilyan 19.8 da gwamnatin Mohammed Abubakar ta yi, kwanaki kwadan kafin ta mika mulki ga gwamna Bala Mohammed na PDP.
An ruwaito cewa a yanzu akwai naira bilyan 11 a cikin asusun ajiyar na gwamnatin jihar Bauchi.
Mai Shari’a Taiwo ya umarci EFCC ta yi duk wani binciken da za ta yi ta kammala a cikin kwanaki 21 kuma ta sanar da Gwamnatin Bauchi matakin da za ta dauka bayan kammala binciken.
An dage shari’ar zuwa ranar 3 Ga Satumba.
Tun da farko, lauyan EFCC ya shaida wa Mai Shari’a cewa hukumar na binciken wata harkalla da asarkalar kudade inda suna da lambar asusun ajiyar kudaden jihar Bauchi da ke a bankin FCMB ya rika fitowa a wurare daban-daban da aka yi harkar fitar da makudan kudade gab da saukar gwamnatin Mohammed Abubakar.
Lauyan ya ce bincike ya nuna cewa an yi amfani da sunayen wasu kamfanoni na bogi masu yawan gaske an cire kudade daga asusun na gwamnatin jihar Bauchi.
“Ya Mai Shari’a, an cire kusan naira bilyan 19.8 na cakin kudade a daidai kusa da mika wa wannan sabuwar gwamnatin jihar mulki. An rubuta cewa kudaden an biya kwangiloli da su. Amma bincike ya nuna babu wadannan kwngilolin, kuma kamfanonin duk na bogi ne.
Ya kara da cewa kudaden da ya kamata a samu a cikin asusun ajiyar ya kamata a ce sun fi naira bilyan 11 din da ke ciki a yanzu.
Da mai shari’a ya tambaye ko idan an kulle asusun zai iya haifar da tsaikon gudanar da harkokin gwamnati a jihar Bauchi, sai lauyan ya ce hakan ba zai haifar da wata takura daga gwamnatin jihar Bauchi ba.
Ya ci gaba da cewa asusun ba ma shi ne asusun da Gwamnatin Tarayya ke saka wa Jihar Bauchi kason ta da ake ba ta a kowane wata ba ne.
“Akwai wasu asusun daban, shi wannan da za mu kulle kulle kuwa, mun rike shi a matsayin shaidar da za mu gabatar wa kotu mai lamba 23 da 23 a matsayin shaidar mu.” Inji lauya.
PREMIUM TIMES ta ji cewa an cire wadancan makudan bilyoyin kudade ne daga ranar 24 zuwa 28 Ga Mayu, jajibirin saukar gwamna Mohammed Abubakar.
Discussion about this post