Tsohon ministan Sadarwa Adebayo Shittu ya bayyana cewa yayi matukar yin mamaki da yaga babu sunansa a jerin sunayen ministan da Buhari ya nada.
Shittu ya ce bai taba tunanin cewa Buhari ba zai saka sunansa a jerin sunayen ministocin da ya nada ba.
” Ko a mafarki ban taba tunanin Buhari ba zai dawo da ni kujerar minista ba. Sai dai kuma ni dama mutum ne mai tawakkali.
” Na yi tawakkali ga Allah kuma na yarda da hukuncin Allah. Dole in gode wa Allah a matsayina na Musulmi, Allah ke badawa kuma shine ke hanawa. Shi Allan ne ya sa na zama minista ko a wancan lokaci kuma ina mai matukar godiya ga Allah.
” Tun bayan kammala karatuna na fada harkar siyasa, na rike mukamai da dama har zuwa wanda na rike wato na nan kusa wato ministan Sadarwa. Ina yi wa Allah godiya matuka akan haka.
Shittu ya ce yanzu zai koma ya ci gaba da harkarsa wato aikin lauya.
” Na bude ofisoshina a Abuja zan rungumi kaddara in ci gaba da aikin lauya.
Idan ba a manta ba Buhari ya nada Isah Pantami a matsayin ministan Sadarwa.
Pantami ne ya canji Shittu a ma’aikatar sadarwa ta kasa.
Discussion about this post