BAKON DAURO: Yara sama da miliyan 26 na cikin hadarin kamuwa da cutar a Najeriya -NPHCDA

0

Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta kasa (NPHCDA) ta bayyana cewa yara sama da miliyan 26 a jihohi 25 da babbar birnin tarayya Abuja ke cikin hadarin kamuwa da cutar bakon dauro a Najeriya.

Jami’in hukumar Adetunji Adeoye ya fadi haka a taron bita na fara yi wa yara allurar rigakafi a Akure jihar Ondo.

Adeoye ya bayyana cewa a shekarar bana gwamnati zata yi wa yara kanana ‘yan watanni tara zuwa sama allurar rigakafin cutar mai suna ‘Men A’.

“ Allurar rigakafi ne hanya daya da zai samar wa ‘ya’yan mu kariya daga kamuwa da cututtuka kamar shawara,bakon dauro da shan inna da ya addabe mu a kasarnan.

Ya kuma ce hukumar ta horas da ma’aikata domin ganin an samu nasarar yin wannan aiki.

Bayan haka kwamishinan kiwon lafiya na jihar Wahab Adegbenro ya bayyana cewa gwamnati ta ware kudade domin ganin ta inganta kiwon lafiyar mutane a jihar.

Adegbenro ya ce za a rika duba mata masu ciki da yara kanana a asibitocin jihar kyauta bisa ga sabon shirin inshoran kiwon lafiyan da za a fara amfani da shi a jihar.

“ Za a fara amfana da shirin inshoran kiwon lafiya a jihar daga watan Nuwamba.

Ya kuma yabawa kokarin da kungiyar kiwon lafiya ta duniya(WHO), NPHCDA, UNICEF ke yi wajen ganin gwamnati ta inganta fannin kiwon lafiyar jihar.

Bakon Dauro

Bincike ya nuna cewa kwayoyin cutar ‘Virus’ ne ke haddasa cutar sannan rashin daukan mataki game da cutar ne ke yin ajalin yara kanana.

Akan kamu da bakon dauro ta hanyar shakar kwayoyin wannan cuta a iska, yin tari, yawan zama da mai dauke da cutar,sannan cutar kan dauki tsawon kwanaki 14 kafin ya nuna alamu.

Alamun bakon dauro sun hada da zazzabi,tari,mura, kurarraji, rashin iya cin abinci da sauran su.

Malaman asibiti sun yi kira ga mutane da su hanzarta zuwa asibiti da zaran anji ba daidai ba.

Yi wa yara allurar rigakafi a lokacin da ya kamata na daga cikin hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar bakon dauro da sauran su.

Share.

game da Author