Bakon Dauro ya bullo a wasu jihohin Arewa Maso Gabashin Najeriya inda akalla mutane 21,000 suka kamu da cutar sannan 100 suka rasu a dalilin cutar.
Barno, Bauchi, Yobe da Gombe ne jihohin da suke fama da wannan cuta.
Sai dai kuma ma’aikatan kiwon lafiya na jihohin Adamawa da Jigawa sun ce jihohin bayu basu cikin wadannan jihohi.
An fi yin fama da Bakon Dauro a lokacin yanayi na zafi.
Alamun cutar sun hada da zazzabin, Yawan yin atishawa, Idanuwa suyi jajawur, kurarraji, rashin iya cin abinci, yawan yin hawaye da sauran su.
Malaman asibiti sun bayyana cewa yin allurar rigakafi ne hanyar shine mafi dacewa domin kauce wa cutar.
Jihar Barno
Shugaban hukumar cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko na jihar Barno Sule Mele ya bayyana cewa hare-haren Boko Haram na daga cikin matsalolin da ya hana gwamnati iya kawo kaarshe cutar ta hanyar yi wa mutane rigakafi.
Mele ya ce tsakanin watannin Janairu zuwa Yuli mutane 18,204 sun kamu da cutar inda daga ciki mutane 94 suka rasu.
“Hare-Haren Boko Haram ya hana ma’aikatan kiwon lafiya yi wa yaran dake kauyuka da wadanda ke zama a sansanonin ‘yan gudun hijra allurar rigakafi sannan koda yara sun kamu da cutar wannan matsala dai na hana iyaye zuwa asibiti.
Mele ya ce a yanzu haka gwamnati ta fara yi wa yara kanana daga watanin 18 zuwa shekara tara allurar rigakafi a duk sassan jihar.
Jihar Yobe
Shima jami’in hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya ta jihar Yobe Haruna Umaru ya koka cewa babban matsalar da suka yi ta fama da shine hare-haren Boko Haram wajen yi wa yara rigakafin cutar.
Umaru ya ce daga watannin Janairu zuwa Yuli mutane 2,675 suka kamu da cutar wanda a ciki bakwai sun rasu.
Jihar Bauchi
Jami’in kiwon lafiya na jihar Bauchi Bakoji Ahamed ya ce mutane biyu ne suka kamu da cutar a jihar.
Ahmed yace mutane biyu din da suka kamu da cutar na karamar hukumar Dambam dake makwabtaka da jihar Yobe wanda a tunanin mu cutar ya ketaro ne zuwa jihar mu daga can.
Sai dai kuma yace ma’aikatar su ta maida hankali wajen ganin cutar bai yadu ba.
Jihar Gombe
Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Gombe Nuhu Ville ya bayyana cewa mutane 130 sun kamu da cutar a tsakanin Janairu zuwa Yuli a jihar amma babu ran da aka rasa.
“Binciken da muka gudanar ya nuna cewa cutan ya bullo ne a kananan hukumomin Dukku da Gombe sannan ma’aikatan kiwon lafiyar jihar sun tabbata cewa duk wanda ya kamu da cutar ya samu magani kuma ya warke.”
Ville ya ce domin dakile yaduwar cutar gwamnati ta inganta aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko 570 a jihar.