Bada Belin El-Zakzaky nasara ce a gare mu – Yola

0

Shugaban Kwamitin Kamfen din “A Saki Zakzaky”, Abdurrahman Yola, ya bayyana cewa bayar da belin jagoran na su da kotu ta yi wata nasara ce da aka samu bayan jajircewar su da tsayawa tsayin daka wajen daure wa kuntatawa da cin-zalin da aka rika yi musu.

El-Zakzaky da matar sa Zeenata za su tafi asibitin Mandetta ne da ke New Delhi, na kasar Indiya.

“ Saboda mun gani kuma mu ma shaida ne yadda gwamnatin kama-karya ta Najeriya ke kuntata wa al’umma ta hanyar yin watsi da umarni kotu. Wannan kuwa ya kara tabbatar da yadda gwamnatin ke ci gaba da danne wa dan adam hakkin sa.

“ Tsawon lokacin da gwamnatin ‘yan kama-karya ta yi tsare da El-Zakzaky da matar sa, ya sa rashin lafiyar ta kara muni da tsanani, har ta kai tilas su na bukatar gaggawar yi musu aiki a asibitin kasar Indiya.

Jagoran na ‘yan Shi’a dai ya shi da matar sa sun samu raunukan ne a lokacin da sojoji suka kai kazamin farmaki a gidan sa, ranar 16 Ga Dimsamba, 2015.

Kuma tun daga ranar suke tsare a hannun hukuma har yau lokacin da aka bada belin sa.

‘Yan Shi’a uku sun mutu a hannun ‘yan sanda, an ki barin a gana da wasu 15 – AI

Kungiyar Jinkan Dan Adam ta Amnesty International, ta bayyana cewa akalla mabiya Shi’a uku ne suka mutu a hannun jami’an ‘yan sanda.

Amnesty International ta kuma kara da cewa akwai wasu 15 da aka killace aka yi musu tsarewar kare-kukan-ka, domin an ki bari a gana da su.

Jiya Litinin ne kungiyar ta ce cikin 15 din da ba a bari an gana da su ba da ke tsare a hannun jami’an ‘yan sanda, har da kananan yara da su ma ke tsare makonni da dama.”

Wadannan mambobi na IMN na cikin jama’a da dama da aka kama a lokacin da zanga-zangar da mabiya Shi’a masu neman ganin an saki shugaban su Ibarahim El-Zakzaky ta yi muni a Abuja.

Amnesty International ta nemi a gaggauta yin binciken yadda mutanen uku suka mutu a hannun ‘yan sanda.

“ Dole ne Gwamnatin Najeriya ta yi binciken yadda wannan mutane da ke tsare suka mutu sanadiyyar harbin bindiga a lokacin da suke tsare.”

Haka wani bayani ya kunsa wanda AI din ta aiko wa PREMIUM TIMES.

Jiya Litinin ne dai kotun Kaduna ta amince wa El-Zakzaky shi da matar sa Zeenat tafiya kasar Indiya domin a yi musu magani.

Sai dai kuma kotun ta ce za su tafi har da jami’an tsaro da kuma jami’an gwamnatin jihar Kaduna.

Share.

game da Author