BABBAN SALLAH: Buhari ya sauka Daura

0

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sauka garin Daura domin shirye-shiryen bukin babban Sallah.

Buhari ya tashi zuwa garin Daura ne bayan sallar Juma’a a Abuja tare da iyalansa.

Idan ba a manta ba a duk shekara shugaba Buhari kan yi babban Sallarsa ne a garin Daura.

Ana sa ran shugaban ƙasa tare da iyalansa zasu dawo Abuja a mako mai zuwa bayan shagulgulan babban Sallah.

Share.

game da Author