Ba gasa NNNPC ke yi da matatar mai ta Dangote ba – Mele Kyari

0

Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kyari, ya bayyana cewa kamfanin harkokin mai mallakar kasar nan, wato NNPC ba ya gasar neman kasuwa da kamfanin matatar danyen man fetur da Dangote ke aikin kafawa a Lagos.

Maimakon haka, Kyari cewa ya yi NNPC kokarin habbaka ayyukan masu son inganta harkokin tace danyen mai a kasar nan ya ke yi.

Da ya ke jawabi jiya Laraba a lokacin da Aliko Dangote ya kai wa Kyari ziyara a hedikwatar NNPC da ke kan hasumiyar NNPC a Abuja.

Kyari ya fayyace cewa a matsayin NNPC na kamfanin da ke tasarifin albarkatun kasar nan da tattalin arzikin ta, kamfanin na da hakkin mara wa kamfanoni, kamar Dangote Group ya cimma kudirin san a zama mai tace danyen mai a kasar nan. Idan ya yi haka, zai kasance shi ne babban mai fitar da man fetur a kasashen waje.

Cikin wata takarda da Kakakin NNPC, Ndu Ughamadu ya sa wa hannu, Kyari ya tabbatar wa Dangote duk wani mai son harkar inganta kasar nan ta hanyar tace danyen mai za a ba shi damar jaraba sa’a.

Da ya ke jawabi tun da farko, Dangote ya ce makasudin shigar sa harkar tace danyen man fetur a kasar nan, shi ne domin ya hada hannu da NNPC maimakon ya kasance mai gasa da NNPC.

Yace kokarin da gwamnatin tarayya ke yi domin ganin ana tace danyen mai a cikin Najeriya ya sa shi nuna kishin kafa masana’antar tace mai a Lagos.

Dangote ya ce idan aka kammala gina masa’antar, ta ce za ta rika tace gangar danyen mai 650,000 a kullum.

“ Abu mafi muhimmanci shi ne mu buda tare da nazarin yiwuwar yadda za mu hada guiwa da hannu da NNPC wajen tabbatar da ida nufin mu, ba wai mu rika goyayya ko gasa da juna tsakanin Dangote Refinery da NNPC ba.

“ Za mu so NNPC ta kasance ta shiga cikin wannan harkar kasuwancin na mu, mu din ma mu kasance cikin harkar NNPC din. Ina ganin ta haka ne kawai bangarorin biyu kowa zai yi nasarar cin moriyar juna.”

Zai yi nasarar cin moriyar juna.”

Share.

game da Author