Attahiru Jega ya shiga PRP

0

Tsohon shugaban hukumar Zabe, Attahiru Jega ya shiga jam’iyyar PRP.

Shugaban kwamitin dattawan Jam’iyyar, Balarabe Musa ne ya tabbatar haka a Kaduna.

Balarabe Musa ya ce ba tun a kwana-kwanannan bane Jega ya ke tattaunawa da shugaban Jam’iyyar domin shiga PRP din, sai gashi kuma Allah yayi hakan ya tabbata.

Idan na a manta ba Attahiru Jega ne ya gudanar da zabe na farko da wani daga kananan kabilun kasar nan ya dare mulki kasar nan a 2011, sannan kuma shi din ne dai yayi zaben farko da Jam’iyyar adawa ta kada jam’iyya mai ci a Najeriya a 2015.

Ko yaro ka ci karo da a fadin kasar nan ya san wannan suna na Jega.

A karshe Balarabe Musa ya ce kofar Jam’iyyar PRP a bude take ga kowa da kowa ya shigo dimin a yi wannan tafiya da shi.

Share.

game da Author