APC ta goyi bayan farmakin EFCC gidan Ambode, tsohon gwamnan Legas

0

Jama’iyyar APC ta nuna goyon bayan dirar mikiyar yin binciken da jami’an Hukumar EFCC suka kai da sanyin safiyar yau Talata a gidan tsohon gwamnan jihar Legas, Akinwunmi Ambode.

EFCC ta kai farmakin ne a gidan sa da ke Efe, jihar Legas. Sannan kuma ta kai wani farmakin a lokaci daya a gidan shugaban ma’aikatan gidan gwamnati a lokacin mulkin Ambode..

PREMIUM TIMES ta tabbatar da cewa EFCC ta na binciken tsohon gwamnan, kamar yadda kakakin hukumar Tony Orilade ya tabbatar wa wannan jarida.

An fara binciken Ambode ne watanni kafin saukar sa daga mulki a ranar 29 Ga Mayu, 2019.

An kai farmakin ne a gidan Ambode wanda ke garin su, Epew, wajen karfe 9:35 na safe.

Haka nan an shiga gidan tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnatin Legas, wanda gari daya gidan na sa ya ke da gidan Ambode. Kuma su na makwabtaka da juna.

Ana zargin an karkatar da bilyoyin nairori a zamanin mulkin Ambode.

Ko a cikin makonni biyu da suka gabata, EFCC ta kulle wasu asusun bankuna masu cike da bilyoyin kudade, wadanda aka danganta da cewa duk da sunan Ambode ba ne mai asusun ajiyar, to ya na da alaka da su da kuma kudaden da ke ciki.

Sai dai kuma Ambode ya karyata, kuma ya nesanta kan sa da asusun da kuma dukkann kudaden da aka ce su na cikin su.

APC ta goyi bayan kai farmaki

Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC, Lanre Issa-Onilu, ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa farmakin da EFCC ta kai gidan Ambode ya nuna cewa wannan mulki na jam’iyyar APC babu wanda ya fi karfin a bincike shi idan har ana zargin sa da aikata wata harkalla.

Haka Lanre ya shaida wa PREMIUM TIMES da ya ke magana a kan farmakin wanda EFCC ta kai wa tsohon gwamnan na APC na Jihar Legas.

“ A yanzu dai lokaci ya yi da za mu sani cewa gwamnatin APC babu ruwan ta da kai ko wane, idan maganar yaki da cin hanci da rashawa ake yi.

Da aka tambaye shi ko APC na goyon bayan farmakin da aka kai gidan Ambode, sai ya ce, “ Mu ba mu ware wani ko batun matsalar wani mu ce mu na goyon baya ko rashin goyon baya ba. Amma dai mu na fatan zargin da ake yi masa ba gaskiya ba ne. Amma idan gaskiya ne, wannan gwamnatin ba za ta rufa wa duk wani da ya rarumi dukiyar jama’a asiri ba.”

Ya ce ai dama yaki da cin hanci da rashawa na daya daga cikin manyan shika-shikan gwamnatin APC.

Share.

game da Author