A taron Inganta shayar da jarirai nonon uwa da ake yi daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Agustan kowace shekara,(UNICEF) da kungiyar ‘Developing-8 sun yi kira ga kasashen duniya musamman kasashe masu tasowa kan maida hankali wajen inganta shayar da jarirai nonon uwa.
D-8 da UNICEF sun kuma ce kamata ya yi mutane su rungume shayar da jariri nonon uwa da matuƙar mahimmanci domin kiwon lafiyar ƴaƴan su.
A wata takardar da aka raba wa manema labarai a Abuja jami’in bada shawara kuma shugaban fannin kiwon lafiya da kare hakin dan adam na kungiyar D-8 Ado Muhammed ya ce kamata ya yi kasashe masu tasowa su maids hankali matuka wajen tallata ingancin shayar da jarirai nonon uwa.
“Mai da hankali wajen inganta shayar da jariri nonon Uwa hanya ne da zai taimaka wajen inganta kiwon lafiyar mutane musamman jarirai a duniya da bunƙasa tattalin arzikin kasa.
Muhammed yace shayar da jariri nonon uwa mataki ne dake hana yawan mace macen yara ‘yan kasa da shekara biyar da ake fama da.
Bayan haka sakamakon binciken da babbar bankin duniya ta gudanar game da kawar da yunwa ya nuna cewa saka dala daya a hanyar inganta shayar da jariri nonon uwa zai samar da ribar dala 35 wa kasa.
Shugaban UNICEF Henrietta Fore ta bayyana cewa shayar da jariri nonon uwa abu ne da duka duniya ta yi na’am da shi saboda ingancin dake tattare da shi.
Sai dai kuma bincike ya nuna cewa kashi 60 bisa 100 na jarirai a duniya ba a shayar da su nonon uwa yadda ya kamata.
Ta ce hakan na da nasaba ne da rashin mara wa mata baya da wasu wuraren aiki ke kin yi da rashin samar da dokokin da za su taimaka wajen inganta shayar da jariri nonon uwa da wasu gwamnatocin duniya suka ki yi.