Akalla mutane 56 ne aka damke a fadin kasar nan wadanda aka kama wurin zanga-zangar ‘juyin turu’. Haka wani lauya dan rajin kare hakkin jama’a ami suna Inibehe Effiong ya bayyana.
Effiong wanda kuma shi ne lauyan zanga-zangar da ke tsare, wato Omoyele Sowore, ya bayyana tsare wannan adadin ne a shafin sa na Facebook jiya Litinin da tsakar dare.
Ya kara da cewa wannan adadi na su 56 sun hada har da ‘yan jaridar da jami’an tsaro suka kama a wuraren da suka je dauko rahoton masu zanga-zanga daban-daban.
An dai kama Sowore tun ranar Asabar tsakar dare, kwana biyu kafin lokacin yin zanga-zangar da aka shirya yi ta game-gari, wadda suka sa wa suna ‘juyin turu.’
Effiong ya karyata zargin da gwamnatin tarayya ta yi cewa an shirya zanga-zanagar ce da nufin a kifar da gwamnatin Buhari.
Shugaba Muhammadu Buhari dai ya kira yunkurin zanga-zangar da cewa tarzoma ce kuma cin amanar kasa ce.
Ana ganin wannan jawabi da ya yi ne ya kara wa jami’an tsaro kwarin guiwar fatattakar masu zanga-zanga tare da kama da dama daga cikin su, har da wasu ‘yan jarida.
Cikin ‘yan jarida da aka kama har da Ibrahim Danhalilu, tsohon editan labaran siyasa na jaridar Daily Trust.
Sai dai shi Danhalilu an kama shi ne sakamakon wani rubutu da ya yi a shafin sa na Facebook, inda ya nuna goyon bayan a yi zanga-zangar.
Cikin jihohin da aka kama masu zanga-zanga akwai Lagos, Cross River, Ondo da kuma Ogun.
’Yan sanda sun zargi wasu ‘yan jarida da cewa wai su ma su na cikin masu zanga-zangar goyon bayan #RevolutionNow, wato ‘Juyin Turu Kawai.’