An sace shugaban jam’iyyar AA a Abuja

0

Da sanyin safiyar Juma’a ne wasu da ba san ko suwa nene ba suka yi garkuwa da shugaban jam’iyyar AA a bankin Zenith da ke Dutse, babban birnin tarayya, Abuja.

Mai dakinsa, ta bayyana wa wakilin PREMIUM TIMES cewa maigidanta ya tashi da safe inda ya ga an yi ta kwashe masa kudi a asusun ajiyar sa na bankin Zenith din.

Cikin gaggawa sai ya garzaya zuwa bankin da sassafe domin kai musu kukan abin dake faruwa.

Isarsa ke da wuya sai aka kawai wasu a cikin babban mota kirar SUV suka kama shi tun daga waje suka saka shi cikin motan suka tafi da shi.

Matan tace a lokacin da take ba wakilin mu wannan rahoto, tana hanyanta na zuwa ofishin ‘yan sanda ne domin sanar musu.

Idan ba a manta ba jam’iyyar AA ita ce jam’iyyar da tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha ya tsayar da surikinsa takarar gwamnan jihar Imo.

Share.

game da Author