Masu garkuwa sun yi garkuwa da dan majalisar jihar Sokoto dake wakiltar Dange/Shuni a majalisar jihar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Abubakar Sadiq ne ya bayyana haka da ya ke zantawa da manema labarai a Sokoto.
Ya ce masu garkuwan sun far Aminu Bodai tun da sassafe ni inda suka far yi garkuwa da shi.
Sadiq ya kara da cewa tun bayan samun wannan rahoto kwamishinan ‘yan sandan jihar Ibrahim Kaoje ya aika da karin jami’an ‘yan sanda cikin dazukan dake kusa da inda aka arce da Aminu.
Discussion about this post