Wasu likitoci dake gudanar da bincike a cibiyar gudanar da bincike a Massachusetts kasar Amurka sun bayyana cewa sun gano maganin dake warkar da dajin dake kama fatar mutum.
A binciken da suka gudanar likitocin sun gano wannan maganin ne a cikin kwan kaza inda suka yi amfani da sinadarin kwan kazan suka yi wa berayen da suke dauke da wannan cutar allura.
Daya daga cikin likitocin da suka gudanar da wannan bincike, Yanpu He ya bayyana cewa sun kuma gano cewa sarrafa wannan maganin zuwa wani abu da za a iya likawa a jiki ya fi allura ko kuma kwayan magani inganci a jikin berayen.
“ Maganin ya kawar da kwayoyin cutar daji a jikin berayen a cikin minti daya sannan ya samar wa berayen rigakafi daga kamuwa da cutar.
Paula Hammond jagoran likitocin ta bayyana cewa gano wannan maganin da suka yi zai taimaka wa sauran likitoci wajen gano magunguna sauran cututtukan dake kisan mutane a duniya.
Hammond ta ce za su ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da ingancin wannan magani.
“Muna sa ran cewa nan da shekaru uku zuwa biyar wannan magani zai yadu a kasuwanni da kuma asibitocin duniya domin ceto rayukan mutane daga wannan cuta.
Discussion about this post