Ofishin sakataren gwamnatin tarayya ta fitar da jadawalin shirye-shiryen rantsar da sabbin ministocin da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai nada.
Babban Sakatare a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya, Babatunde Lawal, ya bayyana cewa za ayi ganawa ta musamman da sabbin ministocin domin tattaunawa na sanin makaman aiki a ranakun 19 da 20 na watan Agusta.
Ranar 21 kuma gaba daya za a hallara a fadar shugaban kasa inda za a rantasar sabbin ministocin sannan kowa ya san ma’aikatar da zai yi aiki.
Cikin wadanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sun hada da tsohon gwamnan jihar Akwa-Ibom Godswill Akpabio, Babban Lauya Festus Keyamo, tsohon gwamnan jihar Benuwai George Akume da wasu 40.