Shugaban karamar hukumar Shendam dake jihar Filato Alex Nantuam ya bayyana cewa manoman kauyukan Shendam, Dokan Tofa, Angwan Rina, Anguwan Dadi da Kallum sun tafka asarar amfanin gonakinsu a dalilin ambaliyar ruwan saman da aka yi kamar da bakin kwarya.
A dalilin wannan ambaliya an kiyasta cewa mutane sun yi asarar da ya kai Naira miliyan 70.
Nantuam ya fadi haka ne da yake ganawa da dan majalisar tarayya dake wakiltar Filato ta kudu a majalisar kasa, Ignatius Longjan a ziyarar jaje da ya kawo wa mutanen da abin ya shafa.
Da yake jabinsa Dakacin Dokan Tofa, James Langkwap yagodewa Longjan bisa wannan ziyara da ya kawo wa mutanen sa sannan yayi kira ga shi da sauran mutane da su kawo wa mutanen yankin agaji na gaggawa.
Logjan ya bayyana cewa ya ziyarci wannan karamar hukuma ne domin ya jajaenta wa mutanen da suka yi asara dakuma gnin yadda majalisar kasa za ta iya shigowa cikin al’amarin domin sama wa mutanen agajin gaggawa.
Bayan haka yace zai tabbata duk wani taimako ko gudunmawa da mutanen za su samu, ya isa ga hannu wadanda abin ya shafa.