A kafa kotun musamman don hukunta masu satar jarabawa –Tsohon Shugaban JAMB

0

Tsohon Shugaban Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’a ta Kasa, JAMB, ya bada shawarar gaggauta kafa kotun-tafi-da-gidan-ka, wadda kacokan za a dora mata nauyin hukunta masu karya doka da satar jarabawa.

Bello Salim, ya bada wannan shawara ga Shugaban JAMB na yanzu, Ishaq Oloyede, a cikin wata sanarwa da mujallar JAMB ta buga, kuma ta turo wa PREMIUM TIMES.

Salim, wanda Farfesa ne, ya bar shugabancin JAMB cikin 2006. Ya nuna damuwa matuka ganin yadda shari’a da hukunta masu zatar jarabawa ke tafiyar-hawainiya a kotunan kasar nan.

Ya ce tunda ita kanta jarabawar JAMB ta zama a zamanance ta na’urorin intanet ake yi, to kamata ya yi ita ma shari’ar masu karya dokokin JAMB ta kasance a zamanance. Haka Salim ya bada shawara.

Ya ce satar jarabawa matsala ce da ta zama ruwan dare game duniya. Amma abin damuwa ne yadda shari’ar masu karya dokar ke tafiyar-hawainiya.

“Ta yaya za a kama wanda ya yi satar jarabawa cikin watan Agusta, ba za a gurfanar da shi kotu ba, sai cikin watan Oktoba. Sannan kuma idan aka gurfanar da shi, sai mai shari’a ya sake aza wata ranar daban, ya ce a dawo cikin Jannairu domin fara sauraren karar.”

“Ya kamata a karfafa hukuncin nan da doka ta gindaya cewa duk wanda aka kama ya na satar jarabawa, to daurin shekaru bakwai sun hau kan sa.”

Daga nan ya shawarci Hukumar Kula da Aikin Bautar Kasa, NYSC da ta kara kaimi wajen fatattakar masu bautar kasa wadanda ba su cancanta ba.

Share.

game da Author