Likita Tolu Adeleke wanda ya kware wajen kula da masu fama da cutar ƙanjamau ya yi kira ga mutanen dake dauke da cutar da su mai da hankali wajen shan magani maimakon ace wai an zuba wa Ikon Allah ne Ido domin a warke.
Adeleke ya fadi haka ne a shafinsa na Tiwita inda yake cewa ya samu labarin yadda wani haka kawai ya daina shan magani, wai shi Allah kawai zai dogara ga domin samun sauƙi.
Ya ce yin haka jahilci ne sam bai dace ba.
“Tabas dogaro ga Allah shine abin da yafi dacewa sannan yana da muhimmanci amma ƙin shan magani idan mutum na bashi da lafiya da sunan wai yana jiran samun lafiya daga Allah, Jahilci ne matuƙa.
Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne tsohon shugaban hukumar hana yaduwar cutar kanjamau ta kasa (NACA) Sani Aliyu ya yi kira ga masu fama da cutar kan daurewa wajen shan magungunan su.
Aliyu yace rashin shan maganin cutar na haddasa matsaloli da dama wanda kan iya kawo wa gwamnati matsaloli wajen kawar da cutar.
Ya ce rashin shan maganin cutar na hana cutar warkewa sannan yana hana magani yin aiki a jikin mai dauke da cutar.
Aliyu yace domin guje wa irin wadannan matsaloli ne yasa yake kira ga gwamnati data karfafa dokar kare hakin masu fama da cutar domin samun nasara a burin da suka sa a gaba.
Discussion about this post