Daruruwan mazauna ƙauyen Jirrawa ne suka dunguma zuwa gidan gwamnatin jihar a fusace inda suka mika wa jami’an gwamnati gawan wani yaro mai suna Shafiu Inusa da mahara suka kashe a gona.
Jagoran tawagar wadannan mutane mai suna Muntari Abdullahi ya bayyana cewa kashe-kashen ne ya ishe su haka nan yasa suka ɗauko gawar Shafiu zuwa fadar gwamnati a Gusau.
Ya ce sun zo fadar gwamnati a Gusau ne domin su bayyana wa gwamnati cewa har yanzu kashe-kashen bai tsaya ba a jihar.
” Mahara ne suka iske Shafiu Inusa a gonan mahaifinsa da mahara suka kashe watannin uku da suka wuce yana zuba taki a gonan. Sai daya daga cikin maharan da ya riga isowa ya ce musu da su gudu su bar gonakin su, shi kuma Shafiu ya ki tafiya.
” Kafin kace wani abu sauran maharan sun iso wurin. Suka buɗe wa Shafiu wuta nan take ya rasu. Dama kuma watanni huɗu da suka wuce maharan suka kashe mahaifin sa a wannan gonan. Yanzu haka matan marigayin na nan na yin takaba.
Muntari ya ce bayan haka sun biyo mutane cikin gari suna harbewa. Ya ce ko a hanyarsu ta zuwa Gusau an rika musu waya ana cewa an kashe mutane a wasu ƙauyukan.
Kwamishinan ƴan sandan jihar Usman Nagogo ya bayyana cewa wannan kisa ya tada masa da hankali matuka yana mai cewa lallai jami’ansa za su shiga wadannan dazuka domin farautau waɗannan miyagun mutane.
Baya ga haka Nagogo ya ce akwai yarjejeniya da suka yi da ire-iren waɗannan mutane cewa ba za so riƙa kai wa mutane hari ba amma hakan bai yiwu ba.
Ya ce gwamna Matawalle na iya ƙoƙarinsa wajen ganin an kawo karshen wannan matsala na hare-haren mahara a jihar Zamfara.