Kotun Sauraren Ƙararrkin Zabe ta Jihar Zamfara ta kori ƙarar da aka shigar wadda ake ƙalubalantar takarar Gwamna Bello Matawalle na PDP.
Shugabar Alƙalan kotun su hudu, wato Mai Shari’a Fatima Zeberu ce ta karanto hukuncin bayan rokon da lauyan mai shigar da ƙara yay i a madadin sa cewa ya janye karar.
An kori ƙarar bayan da shi ma lauyan wanda ake ƙarar ya amince da janyewar da mai ƙarar ya yi.
Tun da farko dai an shigar da karar ce a kan INEC, APC da kuma wanda ake kara, wato Gwamna Matawalle.
Haka shi ma lauyan INEC bai tsaya wata jayayya ba, don haka sai kotu ta kori ƙarar.
Kafin nan, masu shigar da kara sun nemi a haramta wa Matawalle hawa kujerar gwamna, domin a cewar su, bai cancanci tsayawa takarar zaben gwamna na 9 Ga Maris ba na Jihar Zamfara.
Sannan kuma sun nemi INEC ta sake wani sabon zaben gwamna a Jihar Zamfara.
A ranar 27 Ga Maris ne INEC ta damka wa Bello Matawalle da sauran ‘yan takarar PDP takardun shaidar cin zabe salum-alum, bayan da Kotun Koli ta zartas da hukuncin haramcin shigar APC takarar zabe a Jihar Zamfara.
An haramta wa APC takara ce saboda zaben fidda-gwanin jam’iyya da aka gudanar ba bisa ka’ida ba.