ZABEN KOGI: ’Yan takarar APC 20 sun ki amincewa da tsarin zaben fidda gwani

0

’Yan takarar zaben fidda-gwani na gwamnan Jihar Kogi, a karkashin jam’iyyar APC, sun yi fatali da tsarin zaben fidda gwanin da uwar jam’iyyar su ta kasa ta ce a gudanar a cikin sirri.

Wadannan ’yan takara su 20, sun sanar da haka ne a cikin wata takadar korafin rashin amincewa da suka aika wa Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole.

Daya daga cikin ’yan katarar ne mai suna Muhammed Ali ya karanta wa manema labarai a jiya Litinin a Abuja.

Ali ya ce sun je hedikwatar APC ta kasa ce domin kawai su nuna rashin amincewar su da tsarin zaben fidda ’yan takara da APC ta ce a gunadar a aasirce a Kogi.

Za a gudanar da zaben gwamna a Kogi da Bayelsa ne a ranar 16 Ga Nuwamba.

“Mu dai ba mu amince da a yi zaben fidda-gwanin takarar Gwamna a asirce ba. Mu na so a kafa kwamitin zabe mai zaman kan sa, ya je Kogi ya shirya zaben fidda-gwani yadda za a bar duk mai sha’awar fitowa takara ya shiga zabe.

Idan ba a manta ba, ranar 5 Ga Yuli ne uwar jam’iyyar APC ta bayyana cewa a yi zaben fidda gwanin takarar gwamnan Kogi a asirce.

Su kuma wadannan ‘yan takara su 20, suka fito a ranar 7 Ga Yuli, suka taru, inda suka nuna rashin amincewar su da wannan umarni na uwar jam’iyyar APC.

“Mu na cike da bacin rai cewa uwar jam’iyya ta bada wannan umarni ba tare da ta ji ta bakin su, ko ra’ayin dukkan masu ruwa tasakin neman tsayawa takarar gwamnan na jihar Kogi a karkashin APC ba.”

Daga nan sai suka kara cewa akwai makarkashiya a umarnin da uwar jam’iyya ta bayar domin a yi zabe a asirce, wanda suka tabbatar da cewa idan aka yi hakan, to abin da zai biyo baya ba zai yi wa jam’iyyar dadi ba.

“Tun da farko ma akwai fa karar da aka shigar a kotun Abuja, inda ake kalubalantar sahihancin shugabancin Shugabannin APC na Jihar Kogi.”

A karshe sun ce ba za su tsaya su rike hannaye kawai, sun a kallo a tauye hakkin dimokradiyya a Jihar Kogi ba tare da sun yi magana ba.

Share.

game da Author