ZABEN KANO: Ganduje da APC sun roki kotu kada ta karbi tulin shaidu 241 da Abba Yusuf ya gabatar

0

Gwamna Abdullahi Ganduje da jam’iyyar APC sun nemi Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Jihar Kano da kada ta karbi tulin kwafe-kwafen shaidun da dan takarar zaben gwamna na PDP, Abba Kabir Yusuf ya gabatar mata.

Ganduje da APC sun gabatar da wannan korafin ne ta hannun lauyoyin su, Offiong Offiong da Ahmad Raji.

Tun da farko sun nuna rashin amincewa a gabatar da shaidun kwafe-kwafe din orijina na sakamakon zaben.

Dan takarar gwamnan Jihar Kano a karkashin PDP a zaben Maris, Abba Kabir Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida, ya gabatar da shaidu 241 a gaban kotun daukaka karar zabe ta jihar Kano.

Abba ya na kalubalantar nasarar Gwamna Abdullahi Ganduje na APC.

Abba da PDP sun maka Ganduje, APC da INEC kotu, inda suka bayyana rashin amincewa da sakamakon zaben gwamna na jihar Kano.

Lauyan Abba da PDP mai suna Adeboyega Awomolo, ya bayyana cewa za su kara kai wasu shaidu domin kara inganta karfin tulin hujjojin da su ke da shi.

Ya ce daga cikin kwafen shaidun da suka gabatar wa kotu, har da orijina din sakamakon na fam din EC8A, EC8B daga zaben wasu mazabu a Kananan Hukumomin Albasu, Bebeji, Bichi, Dambatta, Garun Malam, Gwarzo, Karaye, Kura, Madobi, Nasarawa, Rano, Rogo, Sumaila, Tudun Wada da kuma Warawa da sauran su.

Sai dai kuma lauyoyin Ganduje da INEC da kuma APC, Offiong Offiong da Ahmad Raji, tun da farko sun nuna rashin amincewa a gabatar da shaidun kwafe-kwafe din orijina na sakamakon zaben.

Offiong ya shaida wa kotu cewa don me masu shigar da kara za su kawo buhunan kwafen takardu a kotu, maimakon tantagaryar takardun sakamakon zabe zalla?

Sai dai kuma Shugabar Kotun Daukaka Karar Zaben Gwamna ta Jihar Kano, Halima Shamaki, ta yi watsi da neman a ki karbar shaidar da Abba ya gabatar, wadda Ganduje da APC suka yi ta hannun lauyan su.

A yau Laraba ce ake ci gaba da sauraren kararraki.

Rahotanni sun tabbatar da cewa APC da PDP za su gabatar da akalla shaidu 785 duk a kan zaben gwamnan jihar Kano.

Share.

game da Author