ZABEN 2023: Ba zan nada ‘halifa’ da zai hau mulki baya na ba – Buhari

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da wani shiri na sarari ko na boye wanda zai zabi ‘halifan’ da zai hau mulki bayan kammala wa’adin san a biyu a shekarar 2023 lokacin zaben shugaban kasa.

Ya bayyana haka ne a yayin da ya ke magana lokacin da ya karbi bakuncin ziyarar wasu masana harkokin ilmi a Fadar Shugaban Kasa a Abuja, a yau Talata.

Kakakin Yada Labarai na kungiyar, Bolariwa Bolaji, ya shaida wa Buhari cewa ya kamata ya fara shirin bayyana ‘halifan’ da zai hau mulki bayan sa a zaben 2023.

“ Mu na murna da ganin ka kara samun nasara a zaben 2019, gas hi z aka yi zango na biyu. Nan da shekaru hudu za ka tafi ka huta – to wa zai hau bayan ka?

“Mu na ba ka shawarar ta fito da wasu masu jinni a jika wadanda ke da kishi, ka rika kula da yadda suke gudanar da tafiyar su wajen nauyin da ka dora musu nan da shekaru hudu. Wato idan ka kammala wa’adin ka, kenan ka bar masu jini a jika da za ka damka wa mulki.

Sai dai kuma Buhari ya maida masa amsar cewa har gara ya ki goyon bayan kowa a matsayin wanda zai gaje shi a mulki, don kada ya kawo rudani ga wanda ya nuna ya na ra’ayi din.

“Wannan ma ai abin dariya ne kawai. Ina ganin idan na ware wani na ce shi zai tsaya idan na kammala wa’adi na, zan haifar masa da matsala ce kawai.” Inji Buhari.

Buhari ya bayar da labarin yadda ya ce aka yi masa magudi zaben baya, sannan aka ce duk mai korafi ko ja-in-ja a kan sakamakon zabe, to ya iya garzayawa kotu.

Sai dai kuma ya ce ya gode Allah ya kuma gode wa ‘PVC’, wanda a lokacin takarar sa ta hudu, ya ci zabe yadda babu yadda za a yi a iya murde masa.

“Yawancin matasa a yanzu ba su daukar abu da muhimmanci. Ka dubi ni yadda na yi takara har sau uku, ina karke wa Kotun Koli har sau uku.

“Amma mutane sun dauki ita nasara ba wata abar nema wurjanjan ba. Sun dauka kawai bude ido na yi na gan ni ina shugabancin kasar nan.” Cewar Buhari.

Share.

game da Author