A jiya Litinin ne jam’iyyar PDP ta gabatar wa Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa faifan bidiyon da aka nuna wani babban jami’in INEC , mai suna Mike Igini, ya na cewa hukumar zabe za ta loda sakamakon zaben 2019 a cikin rumbun na’urar tattara bayanai ta ‘server’.
Igini shi ne Kwamishinan Zabe na Jihar Akwa-Ibom. Bidiyon wanda ya yi maganar dai PDP ce ta gabatar da shi a kotu a matsayin shaida.
Gidan Talbijin na Channels ne watsa tattaunawa da Igini, inda ya yi bayanin shirin INEC na loda sakamako a server kafin zaben 2019.
PDP ta gabatar wa kotu bidiyon domin nuna hujjar da ta dogara da ita cewa INEC ta loda sakamakon zabe a ‘server’ kamar yadda ta yi ikirari.
A cikin bidiyon, Igini ya ce za a tattara sakamakon zabe daga mazabu zuwa cikin fam mai lamba EC8A, daga nan kuma sai a rika loda sakamakon cikin na’urar tantance masu rajista, “zuwa cikin ‘server.”
Lauyan PDP ne ya kunna bidiyon a lokacin PDP ta gabatar da mai shaidar ta, Segun Showunmi.
Showunmi shi ne Kakakin Yada Labaran Zaben Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP.
Daga nan kuma sai aka rika yi masa tambayoyi a kan bidiyon wanda ya ke kafa hujja da shi.
Tun farkon shigar da kara dai Atiku ya nemi a ba shi dama ya ga alkalumman da ke cikin server, amma kotu ta hana shi.
Kotu ta kafa hujja da cewa idan ta ba shi damar, to kamar ta yi riga-malam-masallaci ne cewa ta amince akwai server din tun da wuri kafin a gabatar mata da gamsassun hujjoji.
An kuma nuna wani bidiyo na biyu da ke nuna Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu na cewa “ina fatan za a loda sakamakon zabe a server.”
Bidiyo na uku kuma shi ne wanda PDP ta nuna, wanda ya haska wani labari daga Gidan Talbijin na NTA, inda aka ce Hukumar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta ce ba ta da sakamakon shaidar kammala sakandaren da Buhari ya ce ya yi a 1961.
Bidiyon da APC ta Nuna
Lauyan Shugaba Muhammadu Buhari, Alex Izinyon, ya gabatar wa Kotun Sauraren Kararrakin Zaben 2019 wani kwafen bidiyo, wanda aka nuno Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayanin cewa akwai gagarimar matsalar da ake fuskanta wajen loda sakamakon zabe a server.
Gidan Talbijin ne ya yi hirar da shi, kuma aka yada tun wancan lokaci.
Izinyon ya gabarar da bidiyon a lokacin da aka koma ci gaba da yi wa mai shaida na PDP, Segun Showunmi tambayoyi dangane da batun ‘server’.
An nuno Yakubu ya na cewa: Idan ka tuna mun tattauna da Hukumar Sadarwa ta Kasa, NCC cewa mu na samun matsala kan yadda za mu loda sakamakon zabe. Ta ya za mu loda sakamakon zabe inda babu gurabun loda su.”
“Mu na bukatar kara tashi tsaye kafin mu kai gacin samun ci gaban loda sakamakon zabe ta na’urar zamani.”
Haka Yakubu ya bayyana a cikin bidiyon.
Sannan kuma an nuno Yakubu har ila yau, ya na nuna fargabar cewa akwai matsalar barazanar tsarewa ko killace rumbun ajiyar sakamakon zabe ta intanet, saboda gudun barayin zamani, wato ‘hackers’, masu shiga rumbunan ajiya da shafukan jama’a na intanet.