Shin maigida zai iya yi wa matarsa Fyade?
An dade ana ta cece-kuce, mutane na tofa albarkacin bakunan su game da wai ko magidanci a gidan auren sa zai iya yi wa matar sa fyade, duk da cewa halaliyar sa ce.
Wasu na ganin hakan na iya faruwa bisa dalilin idan har mata bata so ba a lokacin da maigidanta ya bukace ta, sannan ya tilasta mata, ya zama fyade tunda ba da sonta bane ya afka mata.
A bisa wadannan dalilai ne muka jefa tambayar ga masu karatu a shafin mu ta Facebook domin jin ra’ayoyin su game da haka, musamman ma’aurata da sauran masu karatu.
A ra’ayin Kabiru Gumel, Nafi’u Nuhu, Aminu Abubakar, Nasir Mustapha, Muhammad Shamran, Bello Tamburan, Faruk Wadata duk sun bayyana cewa bisa ga sharuddan aure babu Kalmar fyade tsakin miji da matar da ya biya sadakinta.
Kabiru Babandi Gumel – “Babu fyade tsakanin miji da mata idan akwai alakar aure tsakaninsu saboda kowa na da hakin kowa na biyan bukatuwar aure. Amma muna sauraron malamai suyi cikakken bayani akan wannan magana.”
Nafi’u Bala Nuhu –“Bai kamata ba,domin inya bukaceta ba zata kiba.Inkuma taki to yayi anfani da ita kawai,sauran bayanai mallamai za su iya fahimtar da mu”.
Omar Naseer Imam – “Hmmm ai bayan daza ayi megida yayi fyade sai dai yasadu da ita badan tanasoba sabida ai yabiya sadaki kuma sadaki ya halatta saduwa”
Aminu Abubakar– “Babu wani Abu kaman feyde a aure idan har aure ne”
Nasir Mustapha- “Anya kuwa in dai aure sukayi taya zai yi mata fyade”?
Muhammad Shamran – “Ta yaya kenan? Ai tunda ta aureshi ai kuma shi kenan domin ta amince da sharudan zaman”
Bello Bello Tamburan Fcbk – “Tayaya? Ai babu ma kalmar fyade a cikin aure musamman tsakanin miji da mata. A addinan ce haramun ne miji ya nemi saduwa da macce ta hana madamar ba tana jini. Amma idan ta hana shi da gangar la’anar Allah ta tabbata a kanta”.
Faruku Wadata – “A iya sanina babu fyade tsakanin ma aurata… Indai bada wani dalili mai karfi ba meyasa zata hanashi saduwa da ita… Kawai idan batason zaman auren sai taje kotu ta raba auren mana”.
Bayan haka Moh’d Musa, Yusuf Al-mujtabah Intai, Ghali Na’Abba sun fayyace ma’anan fyade bisa ga sharadun adini da doka inda suka bayyana cewa hakan na iya yiwuwa idan namiji ya sabawa saduwa ga mace bisa ga adini ko kuma doka.
Moh’d Almahdee Musa – “Ya kamata jama’a a rinka bambance tsakanin al’umar da ta ginu akan ra’ayi da wadda ta ginu akan addini, manzon Allah yace duk matar da mijinta yazo mata sannan ta juye masa baya mala’iku za su tsinemata har gari ya waye,
To amma tsokaci,manzo Allah ya koyar da ladduban zuwan ma mace,misali:
Yace “kada dayanku ya zowa matarsa kamar yadda jaki ke zuwan ma matarsa, ya aika da ‘dan tsako tukuna.
Yusuf Al-mujtabah Intai – “A Dokar Kasa ko a kasar Bature maniji zai iya yi wa matarsa fyade.
Sannan idan shekarun ta bai kai 18 ba kuma aka yi mata aure mijinta ya kwana da ita shima sunan sa Fyade,
Saidai wannan doka ba tada alaka da muslumci ko ka’idun adinin. Don Haka duk Wanda ya aikata daya daga cikin abbuwa biyunnan ba za ace ya yi fyade ba ballantana ace za’ayi masa hukunci”.
Ghali Mukhtar Na’Abba – “Haka na iya kasancewa idan har ka auri macen da shekarunta basu kai 18 ba kuma ka sadu da ita. Ka ga a nan kayi mata fyade
Amman a kundun penal code”
Shehi Ali Ibrahim – “Eh, zai iya! Saboda fyade shine a kwanta da mace ko namiji bada son ransa ko nata ba. Wannan shi ake kira da fyade”.
Sai dai Mohammad Ibrahim yace muddun namiji ya kawo kayan lallaba ko lallashi ba kafin ya sadu da matar sa sannan ta juya masa baya dole ne ya yi mata fyade.
“Kwarai kuwa,saboda wata sai ta tsadance da mijin ta , wata sai miji yakawo kayan lallami , wata mijinta sai ta sakashi aiki , kunga duk lokacin da aka samu akasi a haka a tunanin ku mizai biyo baya”?