Kotun Sauraren Kararrakin Zaben Shugaban Kasa ta aza ranar 4 Ga Yuli ce ranar fara sauraren tantagaryar karar da Jam’iyyar PDP da kuma dan takarar ta Atiku Abubakar, suka shigar kan kalubalantar nasarar jam’iyyar APC da dan takarar ta, Shugaba Muhammadu Buhari.
A ranar 11 Ga Juni ne APC ta janye wani roko da ta yi wa kotu, wanda a farko ta nemi kada a saurari korafin da PDP ta yi.
Da farko APC ta nemi a janye korafin na PDP, domin kamar yadda lauyan APC Lateef Fagbemi ya bayyana, babu sunan lauyan PDP Levi Uzuegwu, a matsayin wanda ya sa wa takardun kofafe-korafen na PDP hannu.
Ganin cewa APC ta nuna rashin amincewa da kwafen korafin da PDP ta shigar, sai PDP ta nuna cewa abin da APC ta yi tamkar wani raini ne ga kotun gaba daya, domin ta shigar da ba’asi a kotu har sau biyu.
Ganin haka ne sai APC ta yi gaggawar rokon kotu cewa ta na so ta janye korafin na ta.
Shi kuma lauyan PDP ya ce ai APC ta rigaya ta makara, ba za ta iya janye kwafen takardun korafin ba.
A kan haka ne shugaban kotun, Garba Mohammed ya zartas da cewa za a fara sauraren korafin a ranar 4 Ga Yuli, ranar Alhamis kenan.
An tsara cewa masu kara na da mintina 10 da za a ba su domin yi wa kotu bayani, su kuma wadanda aka yi kara su na da mintina sgida za za su yi bayanin maida ba’asi.