Gwamnati ta kammala shiri tsaf domin bude kamfanonin sarrafa rogo har guda uku a jihar Abia.
Jami’in cibiyar nazarin kirkiro na’urorin sarrafa amfanin gona ta tarayya (FIIRO) Anthony Chimezie ya sanar da haka a taron yaye manoma 50 da cibiyar ta horas a jihar Abia.
Shirin horas da manoma shiri ne da cibiyar FIIRO ta kirkiro domin horas da manoma dabarun noman zamani da data muhimmiyar rawa wajen farfado da aiyukkan noman kasar nan.
A jihar Abia shirin yafi bada karfi wajen horas da manoma kan yadda za su iya sarrafa rogo ganin cewa rogo na daya daga cikin amfanin gonan da aka fi nomawa a jihar.
Bincike ya nuna cewa daga 1980 zuwa 2016 noman rogo ya karu a kasar nan daga tan miliyan 11 zuwa ton miliyan 57.
Bayan haka Chimezie yace tun da aka kafa wannan cibiyar shekaru 60 da suka gabata cibiyar ta kirkiro na’urorin sarrafa amfanin gona da suka samar da sana’o’In hannu wa mutane 650,000 a kasar nan.
“ FIIRO ta kirkiro na’urorin sarrafa doya da rogo zuwa gari domin tuka tuwon sakwara da alabo.
“ Sannan yanzu muna horas da manoma yadda za su noma amfanin gona domin samun abin dogaro da kai.
Chimezie ya kuma ce a yanzu haka cibiyar FIIRO na kirkiro na’urorin sarrafa amfanin gona a cibiyar su ta Enugu.
Ya kuma yi kira ga manoma da su yi maraba da wannan shiri domin inganta aiyukkansu.