Za a bude asibiti don kula da masu shaye-shaye a jihar Sokoto

0

Gwamnatin jihar Sokoto ta bayyana cewa nan ba da dadewa ba asibitin da zai rika kula da duba lafiyar wadanda suka fada halin rashin hankali ko zautuwa a dalilin ta’ammali da miyagun kwayoyi zai fara aiki a jihar.

Shugaban asibitin Sale Shehu ya sanar da haka a taron samun makawa game da ta’ammali da miyagun kwayoyi da ake fama da shi a kasar nan da aka yi a garin Kware ranan Talata.

Sale ya ce asibitin zai kula da mutanen dake fama da matsalolin shan miyagun kwayoyi a jihar da jihohin dake makwabtaka da jihar.

Ya kuma ce gwamnati za ta fi bada karfi wajen ganin ta horas da isassun ma’aikata domin kula da mutanen da suka fara samun tabuwar hankali a dalilin ta’ammali da miyagun kwayoyi.

“ Mun kuma hada hannu da uwargidan gwamnan jihar domin ganin an horas da masu fama da matsalolin miyagun kwayoyi sana’o’in hannu domin hana su ci gaba da shaye-shaye bayan sun samu sauki an sallame su.

Sale yace za kuma a ci gaba da wayar da kan mutane game da illolin shaye shayen miyagun kwayoyi.

“Za kuma mu bude fanni a asibitin domin horas da mutane yadda za su iya kula da mai fama da tabuwar hankali a dalilin shaye-shayen muggan kwayoyi.

“Yin haka zai taimaka wajen hana yin ta’ammali da mugan kwayoyi sannan da nuna wa mutane wurin samun kula koda sun mutum ya fara zaucewa a kwa-kwalwa.

A karshe shugaban kungiyar lauyoyi mata ‘LARDI’ Rasheedat Muhammad ta bayyana cewa kungiyar su za ta tallafa wa ‘yan jihar da aka kama da laifin shaye-shayen kwayoyi wajen kubuta daga hukunci doka domin turo su su sami kula a wannan asibiti.

Share.

game da Author