‘Yan shi’ah sun harbe ‘Yan sanda uku dake gadin majalisar Tarayya Abuja

0

A cigaba da zanga-zanga da ‘yan shi’a ke yi a babban birnin tarayya Abuja, a ranar Talata masu zanga-zangan sun harbe ‘Yan sanda uku dake gadin majalisar tarayya da nan ne suka dunguma zuwa a yau.

Wakilin PREMIUM TIMES dake wannan wuri a lokacin yace masu zanga-zangan sun harbe ‘yan sandan ne a daidai suna kokarin tattare su daga kutsawa cikin majalisar.

Daya dai kamar a nan take ya sheka lahira, sauran kuma an garzaya dasu asibiti jina-jina.

Share.

game da Author