‘Yan sanda sun kama mahaifin da ya dirka wa ‘yarsa ciki

0

Wani abin tausayi da ban tsoro da ya faru a Asaba jihar Delta shine yadda wani magidanci mai shekaru 39 ya rika kwana da ‘yar cikinsa mai shekaru 15 na tsawon shekaru biyar.

Mahaifin yariyar ya fara kwana da wannan ‘yarsa ne tun tana shekara 10.

Gidauniyar ‘Behind Bars Rights’ ce ta kai karar mahaifin ofishin ‘yan sanda domin a hukunta wannan mahaifi nata.

Shugaban gidauniyar Gwamnishu Harrison yace yarinyar ta gaya musu cewa mahaifiyarta, yayanta da faston cocin su duk sun sani cewa mahaifinta na kwana da ita da yake yi kusan kullum a gidan su.

“Shi mahaifin nata yaka zuba mata maganin barci ne a abinci kafin ya kwana da ita. A duk lokuttan da ta sanar wa mahaifiyarta ko wanta ko kuma faston cocin su basu yarda sannan basu dauki wani mataki akai ba.

“ Ta ce a wasu lokuttan takan farka ne kawai sai taga gabanta face-face da busasshen maniyyi da jini.

Harrison yace a yanzu haka rundunar ‘yan sanda sun kama iyayen wannan yarinya domin gudanar da bincike a kan su.

Ya kuma yi kira ga gwamnatin jiharda ta bude asibiti na musamman domin kula da mutanen da ake yi musu fyade a jihar kyauta.

Share.

game da Author