Hukumar ’Yan Sanda ta bada sanarwar takaita yin zanga-zanga a Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Hulda Jama’a na rundunar ta kasa, Frank Mba ya sa wa hannu a jiya Laraba, ta ce duk wata zanga-zanga da za a gudanar to a yi ta a kammala a Dandalin Unity Fountain da ke gefen otal din Nicon Hilton.
Sanarwar ta ce jami’an tsaron sun fito da wannan tsari ne domin a kara tabbatar da matakan tsaron birnin da kuma harkokin inganta tattalin arziki da sauran ayyukan da ake gudanarwa a cikin sa.
Dukkan masu zanga-zanga a Abuja, daga jiya an shawarce su da su guji muhimman wurare irin su Fadar Shugaban Kasa, Kotun Koli da kuma Majalisar Tarayya.
An kuma gargade su cewa su guji yin dandazo a sauran wurare da ke da nasaba da muhimman bangarorin tsaron kasar nan.
Sai dai kuma jami’an tsaron ba su ce ga dokar da su ke dogaro da itaba har suka kafa wannan tsatstsauran mataki na takaita zanga-zanga a wuri daya.
Sai dai kuma kakakin yada labarai Mba, ya shaida cewa, “wannan takaita doka ta na daga cikin hurumin da doka ta bai wa ’yan sanda wajen kafa ka’idojin yin zanga-zanga, musamman zanga-zangar wadanda aka tabbatar za su iya lalata dukiya, haifar da salwantar rayuka, musamman na wadanda ba masu zanga-zanga ba ne.”
Tuni dai masu rajin kare hakkin jama’a da sauran kungiyoyi suka fara tayar da kayar bayan cewa, doka ta bai wa kowa damar yin zanga-zangar lumana ko a ina a fadin kasar nan.
Sannan kuma sun tunatar da ‘yan sanda cewa Kotun Daukaka Kara ta Kasa ta ce babu dokar ma da ta ce don za a yi zanga-zanga sai an nemi izni daga ‘yan sanda.
Sama da shekara daya kenan magoya bayan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky na gudanar da zanga-zanga a Abuja, domin neman sakin jagoran na su.
Ta baya-bayan nan ta yi muni, inda su ka karya kofar shiga Majalisar Tarayya, sannan kuma rincimi ya haifar da mutuwar mutane biyu da kuma ji wa wasu ciwo, ciki kuwa har da jami’an tsaro.