‘Yan Sanda sun gayyaci sanatan da ya mam-mari mata a kantin saida azzakarin roba

0

Jami’an ‘Yan sanda da ke Hedikwatar Abuja, sun gayyaci Sanata Elisha Abbo, wanda PREMIUM TIMES ta nuno a bidiyo ya na dalla wa wata matar aure mari a cikin kantin saida azzakarin roba, a Abuja.

An umarci Abbo da ya kai kan sa Hedikwatar Babban Birnin Tarayya, Abuja da ke Garki gobe Alhamis da safe, domin tuni an fara binciken cin zarafin gwabzar da ya yi wa matar, wadda aka nuno ta je rabon fada tsakanin sanatan da mai kantin.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Abuja, Bala Ciroma, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa ana kokarin gano dan sandan da ke tare da sanatan a lokacin da ya ke dalla wa matar mari.

Ya ce za a tuhumi dan sandan saboda ya yi tsaye sororo ya na kallon sanata na gabza wa mace mari, amma bai cece ta ba.

“Tuni mu ka fara kwakkwaran bincike a kan lamarin. Mun fara da gayyato dukkan wadanda suka yi fadan da kuma shirin kai ziyara shagon da da aka yi rikicin domin gani da ido.”

Kwamishinan yan sanda y ace jami’an tsaro za su bi diddigin bidiyon da PREMIUM TIMES ta buga domin tabbatar da sahihancin sa.

Tun daga jiya Talata ne milyoyin jama’a ke ta karaji su na kira da a binciki Sanata Abbo tare da gurfanar da shi kotu.

Cikin wadanda suka yi wannan kira, har da Tsahon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, wanda jam’iyyar su daya da Abbo.

Akwai kuma Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode da sauran jama’a da dama.

Ita ma Kungiyar Lauyoyi ta Kasa ta yi kiran da a bincike shi, tare da gurfanar da shi domin a hukunta shi dangane da cin zarafin matar da ya yi.

Ita ma Kungiyar Kare Hakkin Jama’a, wato Amnesty International, ta yi kiran da a gurfanar da shi.

Share.

game da Author