‘Yan sanda masu karbar kudin beli ba su da bambanci da masu garkuwa da mutane – Kwamishinan ‘Yan Sanda

0

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Lagos, Zubairu Muazu, ya bayyana cewa duk wani dan sanda mai karbar kudi kafin a bayar da beli, to ba shi da bambanci da mahara masu garkuwa da mutane.

Muazu ya fadi haka ne a lokacin da ya ke kaddamar ofishin karbar bayanai a hedikwatar CID da ke Yaba, Lagos, a jiya Talata.

A kan haka ne yace hukumar ‘yan sanda ba za ta saurara wa duk wani jami’in tsaro da aka kama ya na karbar kudade idan zai bada beli ba.

Kungiyar Hana Cin Hanci da Tabbatar da Tsarin Doka da Oda ta RoLAC ce ta samar da wurin, yayin da Cibiyar British Council ta ke kula da wajen amma kuma Kungiyar Tarayyar Turaic e ta dauki nauyin kafa shi.

Da ya ke kaddamar da ofishin, Muazu ya gode wa RoLAC, wanda ya bayyana da cewa kafa wannan wuri na daukar bayanai daga zargi ko korafe-korafen da jama’a ke kaiwa ko daga wasu da aka kamo.

Ya ce daukar bayanan su na da matukar muhimmanci a aikin dan sanda a wajen bincike. Domin bayanan da aka dauka su ne ginshikin duk wani binciken da jami’an tsaro za su yi.

Daga nan sai kwamishinan ’yan sandan ya gargadi jami’an sa da kada su sake su jefa kan su cikin kwamagala ko badakalar karbar kudade.

Sai ya ja kunnen su cewa duk wanda aka kama ya na harkalla to ya kuka da kan sa.

“Ina bada shawarar cewa mu kaurace wa cin rashawa, domin ta na bata mana suna kwarai da gaske.

“A ko da yaushe mu na cewa beli kyauta ne. Kuma kyauta din ne. Ina kara jaddada cewa duk wanda aka kama ya na karbar kudi kafin ya bada beli, to ba shi da bambanci da mai yin garkuwa da mutane. Bambancin ku kawai shi ne saboda kowa ya san inda dan sanda ya ke ajiye da wanda ya kama din.

“ Kasar nan ta yi kunci sosai, mu ke da bukatar jama’a, fiye da yadda su ke bukatar mu.”Inji Kwamishinan ’Yan Sanda Mu’azu.

Daga nan kuma ya yaba wa babban jami’in da ke kula da ofishin CID na Lagos.

Share.

game da Author