‘Yan NYSC 22 za su maimaita aikin bautar kasa a Kano

0

Babban Kodinatan NYSC na jihar Kano, Ladan Baba, ya bayyana cewa masu bautar kasa 22 ne za su maimaita aikin su na NYSC a Jihar Kano.

Ya shaida wa manema labarai a Kano cewa dukkan wadanda za su maimaita din su na cikin Rukuni Na Biyu ne na shekarar 22.

Ya yi karin hasken cewa dalilan maimaitawar sun hada da ko dai kin zuwa wuraren da aka tura su yin aikin bautar kasa, akalla tsawon watanni uku a jere ko kuma sauran wasu laifuka da suka zama tilas wanda ya aikata su sai ya maimaita.

Ya ce an yi bikin sallanar masu bautar kasa 1,718 na Rukunin B, Zubi Na 2 a shiyyoyi hudu da ke Bichi, Kura, Wudil da kuma Sakateriyar NYSC da ke cikin Kano.

Ya ce cikin 22 da za su maimaita aikin bautar kasar,18 za su maimaita makonni uku ne zuwa watanni uku.

Ya kuma ce akwai wadanda suka nuna kishi sosai da za a karrama. Daga nan sai ya yaba wa wadanda suka kammala a bisa irin gagarimar gudummawa da suka bayar a fannin ci gaban inganta ilmi, lafiya, noma da kuma wajen gudanar da zaben 2019 da ya wuce.

A karshe ya shawarce su da su da su yi amfani da dabarun koyon sana’o’in hannu da aka koyar da su a lokacin da suke NYSC.

Share.

game da Author