Yadda tayoyin jirgin ‘Air Peace’ suka farfashe yayin sauka filin jirgin Legas

0

Matasalar ta faru ce yayin da mai tuka jirgin, Simisola Ajibola ta ce ta fara jin an shiga canjin yanayi daidai lokacin da su ka kusanci Legas.

Wannan ya sa ta nemi iznin sauka a babban titin saukar jirage na kasa da kasa, ba na cikin kasa da su ka saba sauka ba.

Wasu sassan jirgin sun lalace sosai, ciki har da tayoyin jirgin, wadda har ta gaba ta dagargaje.

Jirgin samfurin Boeing 737, ya taso daga Fatakwal zuwa Lagos da fasinja 133, sai ma’aikata 7.

Wani fasinja da ke cikin jirgin ya bayyana halin da suka shiga a cikin shafin sa Twitter, mai suna @Ariellafitness cewa mai tukajirgin da sauran ma’aikata sun yi kokarin nuna wa fasinjoji cewa babu wani abin damuwa.

Sai dai wannan tabbacin na su bai shiga kunnuwan fasinjojin ba.

Ya yi korafin cewa bayan da jirgin ya tsaya, ma’aikatan sun yi kira da a je a ceci fasinjojin da ke cikin jirgin, amma sai da aka shafe minti 52 kafin a je a sauko da su daga jirgi.

“Ko da jirgin ya lula kasa, sai mu ka ji ya sauka ba shiri, wata kara da gargada sun kacame jirgin ya dira har silin jirgin ya rikito kasa.

Jami’an Kula da Filin Jirgin da kuma Hukumar Kula fa Filayen Jirage NAA duk sun tabbatar da aukuwar lamarin. Amma dai babu mummunan rauni, kuma babu wanda ya rasa rantsa.

Share.

game da Author