Ma’aikatar Aiyukkan Noma da ci gaban Karkara ta koka kan yadda sashen samar da madara na ma’aikatan ke gab da ya zama tarihi a kasar nan.
Tsohon Ministan aiyukkan noma Mustapha Umar ya koka da haka a taron samun madafa wajen samar da madara a kasashen Afrika karo na hudu da aka yi a Abuja.
Umar ya ce wannan sashe na samar da madara ya durkushewa a kasarnan duk da duk da yawan dabbobi da filayen kiwo da ake da su a kasar nan.
Ya ƙara da cewa a kullum akan samar da madara aƙalla lita 50,000 a Najeriya amma ba ya isan mutanen ƙasarnan sai gwamnati ta shigo da madara daga ƙasashen waje.
“Sakamakon bincike ya nuna cewa akan shigo da kashi 60 bisa 100 na madaran da ake amfani da shi a kasar nan sannan gwamnati kan kashe dala biliyan 1.3 domin ganin haka ya tabbata.
“ Shirya wannan taro zai taimaka wajen samar mana da hanyoyin da ya kamata mu dauka domin inganta fannin samar da madara a kasan nan.
Umar yace a wannan lokaci da ake kara bunkasa aiyukkan noma a kasar nan a tuna da makiyaya suma. A samar musu da tallafi matuka domin suma suna cikin waɗanda ke bukatan haka idan har ana so a samu ci gaba a harkar samar da madara a ƙasarnan.
Shi kuwa babban sakataren ma’aikatar aiyukkan noma Sunday Akpan kira yayi ga gwamnati da ta samar da hanyoyi sannan ta yi doka da za su taimaka wajen bunƙasa samar da madara a ƙasar nan.
Shugaban kamfanin dake yin madaran ‘Peak Milk’ Ben Langat yace babbar matsalar dake ci wa wannan fannin tuwa a kwarya shine rashin ababen more rayuwa.
Wadannan ababen more rayuwa sun hada da wutan lantarki,ruwa,tituna da tsaro.
Langat yace samar da wadannan abubuwa da rage farashin harajin da ake karba a wajen masu kiwon dabobbi shima zai taimaka wajen samar da ci gaban da ake bukata.
A karshe ya ce kamfanin su a shirye Take ta hada hannu da gwamnati domin ganin an samar da ci gaba a wannan fannin.