Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshimhole ya bayyana dalilin ziyarar da kai wa Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin sa na shugaban jam’iyya.
Cikin wata tattaunawa da PREMIUM TIMES, Oshimhole ya bayyana cewa abubuwa sun faru a cikin makonni biyu, wadanda su na da kyau ya je ya kara yi wa Buhari bayanin su.
Buhari in ji shi, shi ne shugaban kasa kuma babban jagoran APC, don haka ya na da kyau ya ji abin da jam’iyyar su ke ciki.
Da ya juya kan irin ci gaban da ya ce an samu a karkashin sa, ya nuna cewa jama’a da dama idon su ya rufe ana kushe shi, ba a kallon irin gagarimin nasarorin da APC ta samu a karkashin shugabancin sa.
Tsohon gwamnan na jihar Edo, ya ce a zaben 2015 APC ta kayar da PDP da kuri’u kasa da milyan uku. Amma zaben 2019 a karkashin jagorancin sa, APC ta kayar da PDP da kuri’u kusan milyan hudu.
Sannan kuma ya kara da cewa a zaben 2019 Jam’iyyar APC ta samu ‘yan Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya masu yawa, fiye da na lokacin zaben 2015.
Da ya juya a kan wasu nasarorin, Oshimhole ya ce ya cancanci a ga irin kokarin da ya yi wajen karya lagon siyasar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki.
“Dama na ce za mu tsige shi ko kuma mu karya masa fukafikin siyasar da ya ke faffaka da su. Mu ka je jihar sa mu ka yi masa raga-raga.
“Kun san karfin siyasar Saraki kuwa? Ya na da karfi sosai, amma da mu ka mu ka yi sunkurun siyasar ‘Otoge’ a Kwara, sai mu ka kwace gwamna daga bangaren sa.
“Duk da Saraki ne shugaban majalisar dattawa, mu ka kayar da shi. Mu ka kayar da dan takarar gwamnan sa. Ba shi da sanata ko dan majalisar tarayya ko daya. Yau a Kwara APC ce ko’ina. To idan ba za ku ga kokari na ku jinjina min ba, sai na zama kadandare, na rika zirgiza kai, ina jinjina wa kai na da kai na.”
Wannan nasara ce Oshiomhole ya ce duk fa a karkashin sa aka same ta.
Da kuma ya juya a kan Sanata Ali Ndume, wanda ya bijire wa uwar jam’iyya ya ce sai ya yi takara da Sanata Ahmed Lawan, ya ce fankama ce kawai ba wani abu ba.
“Cewa ya yi dole sai ya tsaya domin ya auna nauyin sa a siyasa. To ya fito, ya hau sikeli amma kuma an gane duk girman sa ba shi da nauyi, buhun dusa ne kawai.
“A tunanin sa sanatoci ‘yan PDP za su zabe shi, who ya sa wasun su suka ce wai sai dai a yi zabe a asirce. Saboda kuma ya na tunanin cewa duk ‘yan APC ma zaben sa za su yi.”
Oshiomhole ya ce abubuwan da suka faru a 2015 ne ya sa suka canja salon takun siyasar nada shugabannin Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya a 2019.
Batun sabbin ministoci kuwa, ya ce bai ga dalilin da zai sa a fara kushe su ba saboda wadansu dalilai kawai.
Ya ce ko shi da ya yi gwagwarmaya a kasar nan, akwai ‘yan Najeriya da dama da bai sani ba.
Discussion about this post