Yadda ma’aikatan kiwon lafiya ke Ƙƴamatar mu a asibitoci – Masu dauke da Ƙanjamau

0

Ƙungiyar masu fama da cutar Ƙanjamau na yankin Kudu maso yamma (NEPWHAN) sun yi kira ga gwamnati da su maida hankali wajen horas da ma’aikatan kiwon lafiya kan yadda zasu rika kula da masu ɗauke da cutar a Asibiti.

Jami’ar kungiyar Abiola Ajani ta kuma kara yin kira ga gwamnati a riƙa shirya tarorruka domin wayar wa ma’aikatan kiwon lafiya kai game da yadda za su riƙa kula da masu fama da wannan cuta.

Ta ce ci gaba da ƙƴamatar masu ɗauke da cutar zai iya kawo cikas a aikin da suka sa a gaba.

“ Akwai wata rana da nake asibiti sai wata mata mai ciki dake dauke da cutar ta zo asibiti domin yin awon ciki, likitar dake yi wa mata awo tace ba zata duba wannan mata ba sai ta wanke hannayen ta.

“Fadin haka da likitar ta yi ya ti min ciwo matuƙa kuma a hakan matan ta tafi gida ba a duba ta ba.

“Allah kadai ya san abin da ke faruwa a wasu kauyuka da jihohin kasar nan idan dai hakan na faruwa a jihar Legas.

Ajani ta kuma koka game da yadda wasu ma’aikatan kiwon lafiya ke kiran junan su da sunayen cututtuka kamar su Ƙanjamau a gaban masu ɗauƙe da cutar a asibiti.

Sai dai kuma a jihar Nasarawa abin ba haka yake ba domin Jami’in kungiyar NEPWHAN a jihar Philip Lokoko ya bayyana cewa ma’aikatan kiwon lafiya a jihar basu nuna musu wariya idan sun je asibiti.

Lokoko wanda matarsa da shi ke dauke da cutar ya ce da zaran sun je asibiti ma’aikatan kiwon lafiya na rawan jikin biya musu bukatun su ba tare da sun karbi taro a hannun su.

Share.

game da Author