Yadda Fastoci, Malamai, Alfa-Alfa ke cin zarafin mabiyan su da sunan addini

0

Fasto Biodun Fatoyinbo ba shi kadai ba ne wanda ya fara yin kaurin suna wajen zargin yin lalata da mata da kuma matan aure masu zuwa ibada a cocin sa.

Duk da cewa a yau ya Litinin ya bada sanarwar janye jikin sa daga gudanar da limanci a cocin sa na dan wani lokaci, wannan bai yaye masa tulin abin kunyar da ya dabaibaye shi, shi da cocin sa na Commonwealth Of Zion Assembly, wanda aka fi sani da suna a takaice, wato COZA.

Janyewar ta sa ta biyo bayan zanga-zangar da mabiya addinin Kirista da dama da kuma masu rfajin kare hakkin mata suka yi masa a cocin sa jiya Lahadi a Abuja da kuma Lagos.

An yi masa zanga-zanga ne biyo bayan yadda wata fitacciyar mai daukar hoto mai suna Busola, matar fitaccen mawaki Timi Dakolo, ta fito ta bayyana cewa Fatoyinbo ba faston kwarai ba ne, domin ya taba yi mata fyade har sau biyu.

Batun lalata da mata ko matan aure ya zama ruwan dare ga wasu masu kiran kan su limaman addinin Kirista da kuma wasu masu kiran kan su malaman addinin musulunci.

Sannan kuma irin wannan zargin lalata ba a yau ko jiya aka fara ba. An dade shekaru aru-aru ana tafka wannan alfasha a tsakanin wasu majibinta kusantuwa da addinai da dama.

LALATATTUN MALAMAI, FASTOCI DA BOKAYE

Sau da yawa an fi jin labarun yadda shaidanun bokaye ke ribbatar mata masu zuwa neman asirin tsibbace-tsibbace ke lalata da wadannan matan.

Boka kan nemi yin lalata da mace ta hanyoyi da dama. Haka kuma da dama wadannan matan kan samu kan su cewa wadannan bokaye sun dirka musu ciki.

Manyan Fada-fada na addinin Kirista, musamman manyan limaman darikar Katolika, wadanda ba su aure komai girman su ko yawan shekarun su, sukan kan raja’a wajen yin lalata da kananan yara maza.

An tabbatar da haka a shekaru baya a Amurka, inda aka samu an yi lalata da kananan yara maza sama da 250,000.

Ko cikin watannin baya sai da PREMIUM TIMES ta buga labarai yadda manyan limaman Darikar Katolika na Fadar Paparoma suka koka kan yadda manyan limaman Kirista ke yawan lalata da kananan yara.

An sha kama wasu lalatattun malaman da ke kiran kan su malaman musulunci su na lalata da mata, kama daga budurwa, zawarawa har ma zuwa matan aure.

A Sokoto cikin shekarun baya an kama wani malami a kan gadon wata amarya, kuma tsirara aka kama shi tare da ita.

Sau da yawa an sha kama malaman Islamiyya na lalata da daliban su wadanda suke kebantuwa da su wai da sunan biya musu karatu.

Kamar yadda ake zargin Fatoyinbo da yin lalata da mata da yawa. Haka wasu malaman da limaman da fastoci da kuma Alfa-Alfa ba a san yawan matan da suka yi lalata da su ba.

A wannan zamani, shigowar intanet da kafafen yada labarai na soshiyal midiya sun rika samar da kafar saurin fallasawa ko tona asirin irin wadannan fasto-fasto da malamai masu aikata badala.

Ko cikin shekarar da ta gabata an rika watsa wani faifan bidiyo, inda wani fitaccen malami ya rika furta cewa: “Yawun bakin budurwa ya na kara kaifin kwakwalwa sosai.” Wannan kuwa ya janyo masa fushin jama’a masu tarin yawa, inda aka rika caccakar sa, ana cewa ya wuce-gona-da-iri matuka.

Sau da yawa wasu malaman coci-coci kan fada tarkon shaidan ne idan aka yi la’akari da irin shigar kananan kayan da mata masu zuwa coci ke yi. wata shigar ba ta da bambanci da shigar da ake yi idan za a tafi gidan rawa ko wani gida da ballagazazzu ke sheke-aya.

Mai yiwuwa tunda jama’a sun fara fallasa irin wadannan jarababbun fasto-fasto, Alfa-Alfa ko malamai, za a fara samun saukin irin wannan girtsewa da suke yi, har suke afka wa matan da ba na su ba.

Share.

game da Author