Ruwa marasu tsafta, rashin tsaftace muhalli, rashin cin abinci masu kara garkuwan jiki na daga cikin hanyoyin dake haddasa cutar kwalara a jikin mutum.
Cutar wanda ke sa kaga ana ta yin bahaya na iya yin ajalin mutum a cikin lokaci ɗan ƙanƙani idan ba a gaggauta ɗaukan mataki ba.
Kadan daga cikin alamomin kamuwa da cutar sun hada da Zazzabi, Amai da zawo, kasala a jiki, rashin iya cin abinci da yawan Suma.
Cutar Kwalara a Najeriya
Sakamakon Binciken da ƙungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi ya nuna cewa mutane miliyan 2.9 na kamuwa da cutar a inda daga ciki mutane 95,000 ke rasa rayukan su duk shekara a kasashen dake tasowa.
Sannan binciken da NCDC ta gudanar ya nuna cewa hukumar ta gano wasu kananan hukumomi 83 a kasar nan da suka fi fama da yawan bullowar cutar akai-akai.
NCDC ta kuma ce Kano,Zamfara da Bauchi na daga cikin jihohin da suka fi fama da bullowar cutar.
A kwanakin baya idan ba a manta ba hukumar ta sanar da bullowar kwalara a jihohin Adamawa da katsina inda akalla mutane 64 ne suka kamu da cutar.
Rigakafin Kwalara
Idan ba a manta ba kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta bayyana cewa zuwa yanzu ta yi wa mutane 377,000 allurar rigakafi cutar Kwalara a jihar Adamawa. Sannan kuma WHO ta kuma gina asibitocin kula da mutanen da suka kamu da cutar na gaggawa a wannan lokacin kuma hakan ya san an samu ragowar wadanda suke fama da cutar da mace mace da aka yi ta fama dashi matuka.
Hanyoyin Kare kai daga kamuwa da Kwalara
1. Tsaftace muhalli.
2. Wanke hannu da zaran an yi amfani da ban daki.
3. A guji yin bahaya a waje.
4. Amfani da tsaftattacen ruwa.
5. Wanke hannu kafin da bayan an ci abinci.
6. Cin abincin dake inganta garkuwan jiki.
7. Yin allurar rigakafi
Discussion about this post