Wani attajiri ɗan ƙasar Chana mai suna Mr Lee ya yi ƙaurin suna a musamman jihohin Kano da Jigawa bisa mamaye wa manoma gonakin nomansu ds yake yi.
Shi dai Mr Lee ya kan haɗa baki ne da jami’an gwamnati wajen yin amfani da ƙarfin iko na gwamnati wajen tilasta wa manoman ƙauyuka saida gonakin su ga shi Mr Lee.
A wani Kamfaninsa dake Kano da ake kira Asian Plastic, a kullum sai kaga ɗaruruwan babura a waje suna neman shiga ko za su samu aikin yi.
Manoma da dama sun rasa filaye nomansu a dalilin ayyukan Mr Lee a musamman wuraren su inda a yanzu haka ya mamaye akalla Hekta 12,000 na fili da yake ayyukansa.
Mr Lee yana da kamfanoni har guda uku da yake aiki dasu sannan kuma dubban ma’aikata ne ke aiki a ƙarshin wadannan kamfanoni.
Wasu da dama an yaudare su ne tare da haɗin bakin wasu dagatai, da hakimai wajen tilasta musu su siyar da gonakin su ko kuma su rasa gonar.
Wasu ma ba siyarwa akan tuntubesu da shi ba, zuwa akeyi a rarraba musu kuɗi kamar kyauta sai bayan sun cinye shi sai ace ai daga yanzu gonakinku sun tashi daga matsayin nasu zuwa na Mr Lee.
Ɗaya daga cikin manoma 192 da suka rasa gonakin su Ishaku Yahaya ya bayyana cewa da farko da an gaiyace su ne zuwa fadar Hakimin Kudu. ” Daga nan sai aka riƙa raba mana ₦20,000 sannan muna saka hannu a takarda duk mun dauƙa watandar siyasa ce da aka saba yi ashe yaudarar mu ne akayi aka mika wa Mr Lee gonakin mu.
Yahaya ya ce da abu taƙi ci taƙi cinyewa fa har fadar sarkin Kano marigayi Ado Bayero sai da aka kai ga zuwa. Sarki ya bada umarnin su koma ginakin su. Amma kuma sarkin na rasuwa sai suka dawo suna lallaɓar monoman da su bada gonakin su suna tuntuɓar su da ₦20,000 sannan wasu kuma da ₦38,000.
Idan ba a manta ba tun a shekarar 2017 ne mutanen ƙauƴuƙan Jigawa suka rika kokawa game da yadda gwamnatin jihar a lokaci ke neman kwace musu gonaki domin mika wa Mr Lee.
Filayen sun hada da na manoman dake kananan hukumomin Suletankarkar, Gagarawa, Taura, da Garki.
Sama da mutane 150,000 ne wannan shire na gwamnati zai shafa wanda zai yi sanadiyyar salwantar filayen manoman yankin da ya kai fadin hekta 12,000.
Manoman sun koka cewa gwamnatin Jihar da Mr Lee ne suka haɗa baki don su malƙaka wa kamfanonin Mr Lee gonakin.
Mazauna garin sun koka da wannan shiri matuka inda suka sanar wa Gidan Jaridar Premium Times cewa filayen da gwamnati take kokarin kwace wa daga garesu filaye ne da suka gada daga kakanni.
Mazauna garuruwan sunce ba za su yarda gwamnati ta nuna musu irin wannan fin karfi ba. Za su tsaya tsayin daka domin ganin hakan bai tabbata ba ko da za su rasa rayukansu ne.
Wani mazaunin kauyen Gaya Muhammed Danu ya ce ” Muna cikin rudani sannan dukkan mu muna cikin zullumi akan wannan shiri da gwamnati ta yi akan filayen mu.
“ Wannan filaye dai mun gaje sune da ga iyaye da kakanni. Muna noma wadannan filaye duk shekara sannan da abinda muka noma ne muke ciyar da kan mu, mu aurar da ‘ya’yan mu sannan mu wadata kan mu da abubuwan da muke bukata.
Danu yace gaba dayan su a wadannan garuruwa da ake kokarin kwace musu filaye sun mara ma wannan gwamnati baya dari bisa dari amma da wannan bakin ciki za su saka musu.
A madadin mutanen yankin, dan majalisa Sani Zorrro ya mika wannan batu a majalisar Wakilai kuma tuni majalisar ta umurci wata kwamitinta da ta binciki maganar ta kuma kawo mata bayanai akan abin da ta binciko.
Sai dai kuma kash shi Zorro ya ce tabbas, ko a wancan majalisar an kamar za a duba abin sai kuma bai yiwi domin jami’an gwamnati sun lallaɓa sun toshe wa majalisar baki abin sai yayi tsit.
“A watan Afrilun 2019 na sake mika wannan kuka nawa da na jama’ar Jihar Jigawa a zauren majalisar.” Inji Zorro.
Karanta labarin a shafin mu na Turanci a nan: http://wp.me/p2LdGt-Xl3