Yadda ake fama da matsalar siyar da magungunan da kwanakin aikinsu ya kare a Najeriya

0

Wani abin ban tsoro da tashin hankali dake faruwa a kasarnan shine yadda masu siyar da magani ke saida wa mutane magungunan da kwanakin aikinsu ya kare.

Sannan koda mutum ya nemi ya nuna wa masu shagon cewa akwai matsala sai su nuna masa cewa babu komai maganin na aiki.

A dalilin wannan matsala mutane da dama na kin shan magani kwata-kwata ganin cewa asaran kudin su kawai suke yi.

Wata mata mai suna Yinka Taiwo ta bayyana cewa a garin Abeokuta ta taba siyan maganin da lokacin aikin sa ya kare a wani babban shagon siyyar da magani.

“Magungunan da na siya a shagon sun hada da maganin ciwon kai ‘Paracetamol’, maganin zazzabin cizon sauro da maganin kara karfin garkuwan jiki.

“Na gano cewa lokacin amfani da magungunan sun kare ne bayan na kusa shanye magungunan sannan ko da na mayar shagon da na siya maganin sai dai hakuri aka bani cewa wai za su iya canja mun.

Haka shima Bidemi Bello ya ce shi kam sai da ya kaiga ya tafi ofishin ‘yan sanda bayan gano cewa wani shagon magani na siyar wa mutane maganin da ya kare aiki ne.

Shin da gaske ne maganin da kwanakin aikin sa ya kare zai iya aiki ko bayan haka?

Bisa ga bayanan da masana kimiyyar hada magunguna ta duniya da kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) suke yi ya nuna cewa magani na dai na aiki a jikin mutum idan har lokacin aikin sa ya kare koda an sha.

Hakan na nuna cewa magani zai iya lalacewa kafin ya kai adadin kwanakin da aka ware na amincin sa saboda ba a ajiye shi a wuraren da ya kamata ba.

Sai dai kuma sakamakon binciken da jami’ar Harvard dake kasar Amurka tayi ya nuna cewa maganin da kwanakin aikin sa ya kare zai iya ci gaba da amfani ko bayan haka. Amma hakan na yiwuwa idan aka yi masa kyakkyawar ajiya.

Binciken ya nuna cewa wai don lokacin da aka saka a maganin ya cika, karfin maganin ne ya ragu kamar daga kashi 100zuwa 80 ko 70 bisa 100 har zuwa wani lokaci mai tsawo.

Abin da Kwararru suka ce

Babban sakataren kungiyar masana magunguna na Najeriya Emeka Duru ya bayyana cewa ba da gangar bane masu siyar da magunguna ke siyar da maganin da kwanakin aikinsa ya kare ba.

Ya ce wannan kuskure ne daga wajen su ganin cewa ba kowani lokaci bane masu shagunan magani ke iya gane adadin yawan magungunan da kwanakin aikinsu ya cika a shagunan su.

Duk da haka Duruy ya lissafo hanyoyin da mutane da masu shaguna za su iya guje wa irin haka kamar haka:

1. A duk lokacin da aka je siyan magani a duba kwalin maganin domin tabbatar da kwanakin da maganin zai kare aiki.

2. A kuma duba kalan kwayar maganin ko ya canja kala ko kuma ya fa fara zama gari ko kuma lalacewa.

3. Kamata ya yi duk mai siyar da magani ya rika duba magungunan da yake da shi domin kau da maganin da lokacin aikin su ya kare.

4. Masu siyar da magani su tabbata suna da wurin ajiya mai kyawun gaske saboda gujewa lalacewar magungunan su.

5. A guji siyan magani a kananan shaguna domin kananan shaguna na cikin shagunan dake siyar da jabbun magunguna a kasar na.

A karshe jami’in hukumar kula da amincin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) Abubakar Jimoh ya bayyana cewa hukumar na iya kokarinta wajen ganin an kawo karshen siyar da magungunan da kwanakin aikin su ya kare ko ya cika.

Share.

game da Author