Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, ya sake rubuta wa Shugaba Muhammadu Buhari wasiƙa, inda a wannan karon ya gargaɗe shi cewa Najeriya ta kama hanyar shiga bala’in ‘katilan-makatulan’, kuma Buhari ɗin ne kaɗai zai iya hana ƙasar faɗawa cikin wannan mummunan bala’i.
Obasanjo ya ce kashe-kashe da rikice-rikice na ci gaba da zame wa Najeriya bala’i, ga kuma babbar matsalar yadda ƙabilanci ya ruruta wuta tun bayan hawan Buhari mulki, shekaru huɗu da suka gabata.
Obasanjo ya ce an shafe shekaru masu yawan gaske rabon da Najeriya ta samu kan ta cikin irin wannan masifa da ake fama da ita.
Idan ba a manta ba, cikin wasiƙar da ya rubuta masa, ya shaida wa duniya cewa Najeriya fa ta kamo hanyar afkawa cikin kashe-kashen da idan ba a yi da gaske ba, to zai yi wuya a iya kashe gobarar.
Muhimman Saƙonni 10 da Wasiƙar Obasanjo Ta Ƙunsa
1 – Rugujewar Haɗin kan Kasar nan
Zan yi magana ne dangane da halin ko-a-mutu-ko-a-yi-rai da mu ke ciki, wanda ya shafi kasar mu baki ɗaya. Wannan matsala an bar ta ta na ta kara ruruwa, har ta ci karfin ginshikan da suke rike da wannan kasa tun lokacin da aka kafa ta. Tuni tubulan da suka gina hadin kan kasar nan an fara ruguza su.
Na shiga damuwa da tsoro sosai ganin cewa a yanzu tura ta kusa kaiwa bango, mun kusa kaiwa inda ba za mu iya jan linzami mu tsaida bala’in da ka iya tunkarar kasar nan ba.
Dole ne na nuna damuwa ta, domin a matsayi nan a dan Najeriya, a yanzu haka da tabon raunin Yakin Basasa Zan mutu a jiki na. Haka shi ma da na da tabon raunin yakin Boko Haram zai mutu a jikin sa.
2 – Yanke Ƙaunar Samun Tsaro Daga Gwamnati
Idan fa jama’a ta yanke kauna daga tunanin samun tsaro daga gwamnati, to sai su bi duk wata hanyar da su ke ganin cewa ita ce mafitar nemar wa kan su tsaro. Ko dai mutum ya nemi tsare kan sa ko ta halin kaka, ko kuma gungun jama’a su nemi hanyar tsare kan su ko ta wace hanya. Kowa sai ya nemi ta sa da za ta iya fisshe shi kenan.
3 – Ƙaryar An Kakkaɓe Boko Haram
Sama da shekaru goma kenan ana fama da Boko Haram. A cikin shekarun nan goma kuwa, hudu a cikin gwamnatin ka aka shafe su. A kullum Boko Haram sai ta’asa su ke yi, duk kuwa da ƙaryar da gwamnatin ka ke ta kantarawa cewa an gama da Boko Haram.
Kalaman da Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya ya yi kwanan nan, inda yayi korafin cewa sojoji ba su da kuzari ko kishin yaki da Boko Haram, wata magana ce da amsa kan ta da kan ta dangane da halin da ake ciki a kan Boko Haram.
Duk ma abin da ka ga dama ka je ka ci gaba da fada wa mutane, amma dai kowa ya sani cewa Boko Haram na nan daram, kuma a kullum su na kashe mutane, su na sace mutane da yin garkuwa da su, su yi fyaɗe, kuma su na kama mutane a matsayin bayi su na sayarwa. Wasu kuma su na tilasta su shiga harkar Boko Haram, ta hanyar ɗana musu bam domin su shiga cikin jama’a su na tarwatsa su.
Sannan ina tabbatar maka da sanda da duka kadai ba za a iya korar Boko Haram ba. Saboda ta yaya za ka iya kakkaɓe Boko Haram a Arewa alhali kashi 50 bisa 100 na yankin Arewa maso Gabas ba su da ilmi? Ta yaya za ka kakkaɓe Boko Haram alhali kashi 70 bisa 100 na yankin ba su da aikin yi?
4 – Hargitsewar Rikicewar Makiyaya da Manoma
Rikicin makiyaya da manoma da aka ƙi dauka da muhimmancin magance shi, a yanzu ya yi muni kwarai. Ya tashi daga rikici ya koma hare-hare, samame, garkuwa da mutane da kuma sace su, fashi da makami, kashe-kashe duk faɗin kasar nan.
Babban abin takaicin shi ne yadda wannan ɓarna da ake tafkawa ake mata kallon cewa Fulani ne ke yin ta tare da daurin gindin Fulani manyan kasar nan a yankuna daban-daban.
Karin abin bakin ciki kuma shi ne yadda ‘yan Najeriya da dama da ma wadanda ba ‘yan Najeriya ba ke kallon cewa kai ne aka dora wa dukkan laifin abin da ake aikatawa, a matsayin ka na Bafulatani. Wani lokaci dai hasashe kan zama gaskiya.
5 – Fulani Su Fito Su Faɗi Ƙorafinsu A Zauna a Duba
Akwai bukatar Fulani su fito su fadi dukkan korafe-korafen da suke da shi. Idan su na da hujja, sai a zauna a shawo kan matsalar. Idan akwai wasu kabilu masu wani korafi, su ma su fito su bayyana na su. Sai a zauna a baje komai a kan tebur a nemi maslaha.
6 – Lokaci na Neman Ƙurewa
Bai kamata a riƙa yi wa komai riƙon-sakainar-kashi ba. saboda lokaci na ƙurewa, ko’ina a faɗin kasar nan ba ka jin komai sai koke-kore da korafe-korafen rashin gamsuwa da halin da kasar ke ciki.
Fadar Gwamnatin Amurka da Majalisar kasar sun yi mana hannun ka-mai-sanda cewa ya kamata su kimtsa gidan su kafin ya ruguje. Haka ita ma Majalisar Ingila ta shaida mana.
Ya zama dole su dubi maganganun da suke faɗa mana kuma mu yi tunanin abin da ka iya tasowa ta yadda za mu maida hankali da irin wadannan shawarwari.
7 – Kalaman Ƙiyayya Tamkar Gobarar Daji ce
Idan aka yi turnuku fa ba ka da mai iya tsaida kalaman ƙiyayya da barkewar mummunan rikici. Kalaman ƙiyayya na ƙabilanci wutar ƙaiƙayi ce. Za ta riƙa ruruwa daga ƙasa, a ƙarshe sai ta wo sama ta na ci, ta yadda babu mai iya kashe ta, har sai ta kai ga yin mummunar barna. Idan kunne ya ji, to jiki ya tsira.
Tun bayan kashe Ƴar Shugaban Ƙungiyar Afenifere, kusan sauran yankunan ƙasar nan sun harzuka, su na cewa abin ya ishe su haka nan fa!
Duk lokacin da aka ci gaba da rashin maida hankali ga masu koke-koke, to ƙasar nan ce za ta ji a jikin ta. Ni dai ina sanar da kai Shugaban Kasa kuma Babban Kwamandan Askarawan Najeriya cewa na damu kwarai da wadannan munanan bala’o’i wadanda za a iya kauce musu:
8 – Sakin ragama da akalar Najeriya a hannun ‘yan bindiga wadanda jama’a ke zargin cewa Fulani ne, sai kuma Boko Haram.
9 – Tsoron kada bala’in kashe-kashen ramuwar gayya ya ɓarke a kan Fulani, ta yadda za mu fada irin balbalin bala’in da kasar Rwanda ta taba samun kan ta a ciki. Babu wanda ya taba amanna cewa hakan za ta iya faruwa a Riwanda, amma ga shi kuma hakan ta faru.
10 – Tsoron kada irin wannan kashe-kashen ya koma a kan sauran wasu ƙabilun kasar nan tsakanin su da wasu ƙabilu. Hakan na iya faruwa ta hanyar watsa ji-ta-ji-ta, fargaba, tsoro, barazana da kuma kisan daukar fansa da ka iya ɓarkewa zuwa kisan kiyashi
11 – Fargabar ɓarkewar yamutsi daga wani sashe na ƙasar nan da ka iya watsuwa zuwa sauran sassan ƙasar nan cikin ƙanƙanin lokaci, wanda a ƙarshe zai iya kai ga raba ƙasar nan.
Saboda haka ya faru a Yugoslavia ba da dadewa sosai ba. Idan ba mu tashi tsaye ba, to ɗaya ko duka daga cikin waɗannan bala’o’in ka iya faruwa. Dole mu tashi da addu’a tare da daukar matakin da ya dace a lokaci guda.
Wannan yunƙuri kuwa Shugaban Ƙasa ne zai iya fara yin sa. Amma kuma ba zai iya cin nasara shi kaɗai ba, sai ya samu mataimaka. Masu iya magana na cewa idan ka na cikin washin addar ka, sai mahaukaci ya biyo ta bayan ka, ya fizge wukar daga hannun ka, to ka na bukatar taimakon jama’a da za su hadu domin a karɓe addar a hannun mahaukaci, ba tare da an ji wa wani rauni ba.