Wani ya yi wa mutane takwas wanka da ruwan batir a kasuwa

0

Wani majiya ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa a kasuwar Ugwuagba dake jihar Anambra wani mutum ya kwararra wa mutane takwas ruwan batir.

Majiyar ya bayyana cewa bayan mutumin ya aikata wannan mumunar aiki ya cikawa wa wandonsa iska ya gudu.

“ Mutumin ya aikata haka ne a dalilin ‘yar gadama da ya hadashi da wani abokinsa mai suna Onyeka dake siyar da kayan mota a kasuwar.

Bayan haka kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Haruna Mohammed ya tabbatar da haka sannan yace har yanzu babu wanda suka kama.

“ Mun samu labarin cewa wani ya kwarara wa abokinsa Onyeka Nwachukwu mai shekaru 38 ruwan batir a dalilin gaddamar daya auku a tsakanin su.

“Sai dai kuma ba shi kadai ruwan batir din ya yi wa ta’adi ba domin ya illata wasu mutane bakwai dake kusa da wurin da rikicin ya barke bayan shi wanda aka duldulawa.

Mohammed yace sun kai wadannan mutane asibitin ‘Martin’s Hospital’ dake Ugwuagba domin a duba su. daga bisani Asibitin ta salami shida daga cikin bakwai din daka kai.

Haruna yace tuni har rundunar ‘yan sandan jihar ta fantsama domin kamo wadanda suka aikata wannan mummunar aiki.

Share.

game da Author