Tulin haraji zai samar da kudin shiga, ya inganta tattalin arziki – Fowler

0

An bayyana cewa sabon tsarin Lambar Tantance Masu Biyan Haraji (TIN), zai kara yawan kudaden shigar da gwamnatin tarayya ke samu tare kuma da Inganta tattalin arzikin kasar nan.

Wannan tsari na killace sunayen masu biyan haraji ta cikin kwamfuta, zai samar wa Hukumar Tara Kudaden Harajin Cikin Gida ta Kasa (FIRS) hanyar saukake mata gudanar da aikin tattara bayanan haraji.

Shugaban Hukumar FIRS, Fowler, ya ce wannan tsari na intanet ne, kuma za a rika gudanar da karba ko biyan haraji a saukake ko daga gida ko ofis.

Sannan kuma tsarin zai ba masu karbar haraji damar sanin yawan harajin da wani zai rika biya, ta hanyar yi masa kintacen adadin kudaden da zai biya, gwargwadon ribar da mutum ya samu.

Ya ce a yanzu karni na 21 ake ciki, zamani ya canja, kowane irin bayani ana killace shi ne a cikin rumbun na’urar ajiyar kayayya ki ta intanet.

Hakan ya ce zai kara tabbatar da cewa hanya ce mai sauki tare da kauce wa harkalla a wasu wurare yayin gudanar da aikin tara kudaden haraji a bangarori daban-daban.

Sannan kuma ya ce babbar nasarar da za a samu a karkashin wannan tsari, shi ne kara wa gwamnatin tarayya yawan kudaden haraji da kuma inganta tattalin arziki.

Sannan kuma za a rika tafiyar da tsarin tattara kudden haraji da biyan kudaden a cikin tsari da natsuwa.

Share.

game da Author