TSARO: Hukumar NSCDC zata tura jami’ai 1,500 gonaki

0

Hukumar tsaro na ‘Sibul Difens’ NSCDC ta kammal shiri tsaf don tura jami’anta dazuka domin samar wa manoma da makiyaya tsaro daga hare-haren ƴan ta’adda.

Hukumar ta yi haka ne a ƙarƙashin shirin gwamnatin tarayya da ma’aikatan ayyukan gona mai suna ‘Agro Rancher Scheme’.

A ƙarƙashin shirin hukumar zata tura ma’aikata 1500 cikin dazuka domin daƙile ayyukan mahara da masu tada zaune tsaye a gonaki.

Shugaban hukumar, Abdullahi Muhammadu ne ya sanar da haka da yake zantawa da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Maiduguri, babban birnin jihar Barno, a cikin makon da ya gabata.

Ya ce wannan shiri an tsara shi ne domin samar da tsaro a gonaki da wuraren da makiyaya ke kiwon su. Bayan haka aƙalla jami’ai 2500 ne muka ƙeɓe domin wannan aiki a zangon farko.

Muhammadu ya ce hukumar za ta horas da ma’aikata 750 na tsawon makonni biyar kafin ta tura su. Za a tura jami’ai zuwa jihohin Katsina da wasu jihohin dake fama da ayyukan maharan.

” Za a horas da waɗannan jami’ai dabarun samarda tsaro a rugagge, yadda za su riƙa gane mutanen banza da kamo su da yadda ake samar da taimakon gaggawa idan ko an samu rauni da sauran su.

Bayan haka Muhammadu ya ƙaryata rahotanin da ake ta yaɗawa wai mahara na sace manoma a gonakinsu. Ya ce hakan ba gaskiya bane

Shugaban hukumar tsaron ya ce wannan shiri zai samar da tsaro a rugaggen Fulani 250 dake faɗin ƙasar nan.

Share.

game da Author