Kotun dake sauraren kararrakin zaben kujerar sanatan Kaduna ta Tsakiya, ta bayyana cewa nan bada dadewa ba zata yanke hukuncin karar da dan takarar PRP, Shehu Sani ya shigar yana kalubalantar Uba Sani na jam’iyyar APC a matsayin zababben sanatan Kaduna ta tsakiya.
Idan ba a manta ba, hukumar zabe ta bayyana Uba Sani a matsayin wanda ya yi nasara a zaben sanata da akayi a watan Fabrairun 2019.
Bayan bayyana sakamakon zaben ne, Shehu Sani na jam’iyyar PRP yayi watsi da wannan sakamako inda ya ce an tafka magudi a kananan hukumomin dake karkashin wannan shiyya da aka gudanar da zabe.
Alkalin Kotun A. H Ibrahim ya ce nan ba da dadewa za a yanke hukuncin wannan shari’a.
Lauyan Sanata Uba Sani, Frank Igbe ya bayyana cewa wannan kara bata a hurumin da ya kamata ma a saurare ta. Ya yi kira ga kotu ta yi watsi da wannan kara kawai a huta.
Shi ko lauyan Shehu Sani kira yayi ga kotun da ta ba da dama a sake zabe a wannan shiyya kawai ko kuma ta mika wa Shehu Sani kujerar Sanatan Uba ya hakura.