TAMBADA A SAUDIYYA: Mawakiyar Amurka Nicki Minaj zata yi wasa a Jedda

0

Niki Minaj da ta shahara wajen yin rawar murguda duwaiwai sannan rabi tsirara da fetsarewa zata yi wasa a kasar Saudiyya.

Wannan shine karo na farko da za a irin wasa na butsarewa a kasar.

Minaj da wasu mawaka daga kasar Ingila za su nishadantar da mutane da a filin wasa na Sarki Abdallah dake Jedda.

Mutane da dama na yin Alla tsina da wannan shiri na gwamnatin kasar Saudiyya cewa shirya irin wannan buki bai kamata a ce kasa kamar Saudiyya za ayi shi ba, inda ake zuwa aikin Hajji sannan kuma a wannan kasa ne Kabarin Annabin Tsira Mohammadu SAW yake ba wai kuma za a yi irin wannan tambadewa a ciki.

Masu shirya wannan buki sun ce ba za a siyar ko a sha giya ko muggan kwayoyi a wannan wurin rawa ba.

Wasu daga cikin kawaye, da abokan Minaj suna ja mata kunne cewa kada ta amsa wannan gayyata.

Share.

game da Author