Kungiyar likitocin jinkai (MSF) dake aikin jinkai a yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya ta yi kira ga gwamnati da ta gaggauta kawo dauki wa mutanen dake wannan yanki cewa taɓuwar hankali na neman ya zama ruwan dare a yankin.
MSF ta bayyana haka ne a wani takarda da ta raba wa manema labarai a Maduguri.
A dalilin rikice-rikice, annoba da bala’o’in da ake fuskanta a yankin ne yasa yanzu fa mutane da dama sai zarewa suke yi.
MSF ta yi kira ga gwamnati cewa ya yin da take daukan matakan samar da dauwamammen zaman lafiya a yankin kamata ya yi ta dauki matakan kula da mutanen dake fama da tabuwar hankali.
Idan ba a manta ba a 2017 ne wani babban likitan kwakwalwa Ibrahim Wakama ya sanar da dabarun da suka koyo a kasashen Burundi da Rwanda domin yadda za’a shawo kan matsalar tabuwar hankali da dayawan mutanen arewa maso gabas ke fama da shi saboda ayyukan Boko Haram.
Likitan ya fadi hakan ne a wata hira da yayi da PREMIUM TIMES a taron da kungiyar ‘Development Research and Projects Center DRPC ta shirya a Abuja.’
Ya yi bayanin cewa abin da likitocin suka tanada domin shawo kan wannan matsalar sun hada da ma’aikata, dabarun yadda za’a shawo kan matsalar da kuma kudaden da suke bukata domin hakan.
Ya ce an turo marasa lafiya asibitin su dasu ka kai 1654 sannan kashi 65 daga cikin su mata ne kuma har yanzu da mutane da dama wadanda suke fama da matsalar da ba’a San inda suke ba.
Likita Wakama ya ce matsalolin da suke fama da su shine na karancin kudaden da suke bukata domin siyo kayayyakin aiki, sannan gwamnati har yanzu bata bada nata gudunmawar ba, kuna wasu kungiyoyin da suka saba taimaka musu sun fara janye taimakon na su saboda rashin kudi.
Wasu kwararu likitocin kwakwalwa kamar su Mustapha Gudaji, Faltama Shettima da suka halarci taron sunyi kira ga gwamnati da dasu taimaka domin ganin an samo mafita akan wannan matsala.