Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya nada sabbin shugabannin ma’aikatun jihar.
Kakakin gwamna Ganduje, Abba Anwar ya sanar da haka a takarda da ya fitar daga fadar gwamnatin jihar ranar Talata.
Wadanda aka naɗa sun haɗa da:
1 – Abdalla Pakistan – Shugaban Hukumar Alhazai ta jihar Kano
2 – Aliyu Musa Aliyu – Darekta Janar na Hukunar Hisba
3 – Halima Rabi’u Abdullahi – Babban Sakatariya na Hukumar Ilimi na Bai ɗaya.
4 – Gali Sadiq – Shugaban gidan Radiyon Jihar Kano.
5 – Ibrahim Bichi – Babban Sakataren Ɗakin Karatu na Jihar Kano
6 – Sagir Sadisu Buhari – Darekta Janar na ma’aikatar Bincike da Adana.
7 – Lawan Sabo – Babban Manajan gidan jaridar Triumph
8 – Sa’a Ibrahim – Darekta Janar gidan Talabijin din Abubakar Rimi (ARTV)
9 – Jibrilla Mohammed – Babban Manajan Kamfanin kula da kadarorin jihar Kano.
10 – Ibrahim Galadima – Shugaban Hukƴmar Wasanni na jihar Kano.
11 – Sakina Yusuf – Shugaban Kotun sauraren ƙararrakin matsalolin Hajji.
Discussion about this post